Connect with us

LABARAI

Lauyar Da Ta Kashe Mijinta: ’Yan Sanda Sun Ce Da Gangan Ta Siyo Sabbin Wukake

Published

on


Wata lauya mai zaman kan ta a garin Legas mai suna Udeme Odibi, wadda ta daba wa mijinta mai suna, Otike Odibi, wuka har ya mutu ta amsa laifin cewar, lallai ita ta aikata wannan danyan aikin.

‘yan sanda sun bayyana cewa, lauyan ‘yar shekara 47, tayi wa mahaifiyarta waya inda take gaya mata abin da ta aikata na kashe mijin nata.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar Legas, Edda ‘yanjarida a ofishinsu daka Ikeja, ya ce, wanda ake zargin ta kuma aika wa ‘yar uwarta sako ta kafar WhatsApp kafin ta aikata danyen aikin kashe mijin nata.

Kwamishinan ‘yansanda ya kuma ce, wanda ake zargin ta sayi wasu sabbin wukake wanda daga ciki ta zabi wanda tayi amfani dashi wajen kasha mijin nata dan shekara 50 a duniya.

A ranar Alhamis ne, Udeme ta kashe mijin nata da wuka a gidansu dake unguwan Diamond Estate, Sangotedo, Ajah.

Bayanin ya nuna cewa, ta kuma yanke al’auransa ta dora a hannunsa kafin ta caki kanta da wukan a ciki. Ita dai Udeme, bata mutu ba amma said a aka kai ta asibiti don yi mata magani.

An ruwaito cewa, marigayi Otike ya kira wasu makabtansa da kanuwarsa da kuma mahaifiyarsa ta waya yana musu bayanin cewar, matarsa na barazanar kashe shi.

An kuma ruwaito cewar, shekarar su uku kenan da aure amma basu samu haihuwa ba, sai dai zaman nasu cike yake da tashin hankali da rikice-rikice.

Kwamishinan ‘yansanda ya kuma kara da cewa, zarge-zargen fasikanci da suke wa juna na cikin matsalolin da aure nasu ya fuskanta.

Ya ce, “A ranar da abin aya faru, wanda ake zargin ta aika wa sirikanta sako ta kafar WhatsApp tana korafin halin da suke ciki da mijin nata, tana kuma neman addua’a, ta kuma nemi Allah ya gafarta mata.

“Wanda ake zargin mai suna, Udeme Odibi, tayi ikirarin aikata laifin, inda ta kira mahaifiyarta tana sanar da ita cewar ta kashe mijin nata, wanda ake zargin dai ta kwalawa mamacin wani kwano ne a kai kafin ta daba masa wuka”

Imohimi ya kara bayyana cewa, bayan da Udeme ta fasa cikin mamacin, bata nemi taimakon makabtan taba, wanna n na nuna lallai wanda ake zargin ta shirya kashe mijin nata ne kai tsaye” kwaminshinan ‘yansanda ya kara bayanin cewa, “Wanda ake zargin ta sayi sabbin wukake da ta yi amfani dasu wajen aiwatar da wannan kisan, ta kuma tattara dukkan takardunmakaratar ta, ta kuma yi shirin tafiya kasar Birtaniya ranar Alhamis ta kanfanin jirgin Birgin Atlantic.

“Binciken gawar mamacin na gudana a halin yanzu a asibitin kotarwa na jami’ar Legas, yayin da jam’an mu na kuma ci gaba da sauran bincken, da zaran an kammala cikakken bincike za a sanar da mutane halin da ake ci”

Haka kuma hukumar ‘yansandan sun sanar da maka wata mai suna Gift Mike da zargin kashe masoyinta mai suna Daniel Grant, dan kasar Afrika ta kudu.

Bayani ya nuna cewa, an tsinci gawan Grant ne dan shekara 50, a mace a safiyar ranar Lahadi a wani otal mai suna Emerald Cobe dake kan titin Sinari Daranijo a unguwar Bictoria Island dake Legas.

Manema labarai sun gano cewa, an ga gawar mamacin ne a ban dakin otal din makale a sama yayin da kafafuwansa ke lilo a kasa.

Da kwamishinan ‘yansanda ke karin bayani, ya ce, yanayin da aka ga gawar da hujjojin da suka gani a inda aka ga gawar ya nuna karara cewa kisa aka yi.

Ya ce, tuni aka mika kara zuwa babban ofishin ‘yansanda masu binciken manyan laifuka dake Yaba domin gudanar da cikakken bincike.

Kwamishinan ‘yan sanda ya kara cewa, “Wani mai suna Abu Ismail, shugaban ptal din Emerald Cobe ya kawo koken cewar, sun ga gawar wani mai mu’amala dasu a cikin dakin otal din da alama kuma an rataye shi”

“Ya bayyana mana cewa, ranar 5 ga watan Mayu marigayin dan kasar Afrika ta kudu da budurwarsa mai suna Gift Mike, suka shigo otal din, inda bayan sun yi tatil da giya sai suka tafi wani unguwan da bamu sani ba amma sun dawo da kamar karfe 1.30 na dare inda suka shige dakinsu.

“Da kamar karfe 1.30 na dare sai busurwar wato Gift Mike, ta tashi ta kuma lura ba marigayin a cikin dakin, daga baya ne ta ganshi a rataye a cikin ban dakin, ihun data yi ya ma’aikatan otal dacsauran jama’a suka taru inda daga baya aka kira ‘yannsanda”

“Jami’anmu masu bincike karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yansanda daga ofishinmu na Yaba sun gudanar da binciken gaggawa inda nan tae suka damke budurwar tas domin yi mata tambayoyi”

A halin yanzu gawan mamaci na babban asibitin Lagos Island domin ci gaba da bincike.

 


Advertisement
Click to comment

labarai