Connect with us

LABARAI

Jam’iyyar APC Za Ta Sake Kafa Mulki A Jihar Katsina Cikin Sauki —Mai Masaka

Published

on


Bayan kammala zaben mazabu na jam’iyyar APC a jihar Katsina bayanai ke fitowa a bakuna daban daban game da yanda aka gudanar da zaben, gaba daya bayanai sun nuna cewa, an samu cikkaken nasara a tsarin yadda aka gudanar da zaben, hakan kuma yasa wasu ‘yan jam’iyyar ked a ra’ayin cewa, lallai jam’iyyar za ta sake kafa mulki a zabar mai zuwa na 2019 a jihar cikin sauki.

Alhaji Sani wanda aka zaba a matsayin Ma’ajin jam’iyyar a karamar hukumar Faskari, wanda aka fi sani da suna Sani Masaka wanda shima yana daya daga cikin sabbin shuwagabannin da aka zaba kuma shi ne shugaban jam’iyar APC a yankin mairuwa ta karamar hukumar Faskari.

Ya bayyana nasa ra’ayin gameda shi wannan zabe inda ya ci gaba da cewa babu shakka jam’iyyar APC a Nijeriya ta taka rawar gani a wadansu jihohi musamman a jihar Katsina karkashin jagorancin Alhaji Aminu Bello Masari, musamman ganin aiuyukan ci gaba rayuwar al’umma da aka gudana a cikin shekaru na mulkin APC.

Ya kuma kara da cewa, bisa ga kudirin shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari na ciyar da kasan nan gaba ta kowane bangare in Allah ya yarda sai Nijeriya ta komo sahun farko da zaman lafiya da kuma ci gaban al’umma

Alhaji Sani Masaka ya ci gaba da cewa, a kan haka ne yake yabawa shugaban kasa da gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da sauran gwamnonin jam’iyar APC a Nijeriya musamman wadan da suke kawo sharudda da zasu kawo zaman lafiya da abubuwn ci gaban jama’a da sauran makamantansu ya kara da cewa Allah ya taimaki shugaban Nijeriya game da wadannan kyawawan abubuwan da yakeso ya kawo wa kasar nan.

Sannan ya ci gaba da shawartar ‘yan siyasa musamman masu rike da madafun iko dasu rinka yin koyi da irin wadannan halaye na mai girma shugaban kasa domin a kawo karshen duk wani abu da zai kawo tashin hankali a kasar nan.

 


Advertisement
Click to comment

labarai