Connect with us

LABARAI

Gwamna Masari Ya Yi Ta’aziyar Khalifa Isyaku Rabi’u

Published

on


Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi ta’aziyar rasuwar Sheihk Isyaku Rabi’u Kano wanda ya rasu shekaranjiya yana da shekaru 90 a duniya tare da bayyana rasuwar a matsayin wani babban rashi ga Najeriya baki daya.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamna Masari akan hulda da ‘yan Jarida, Alhaji Abdu Labaran Malumfashi ya sanyawa hannu ya rabawa manema labarai a Katsina.

Alhaji Aminu Bello Masari ya ce an sake samun wani baban gibi kwanaki uku da rashin baban limamin Katsina, marigayi Liman Malam Lawal sai kuma ga rasuwar Sheihk Isyaku Rabi’u Kano.

Gwamna Masari ya ce rasuwar Khalifa Isyaku wani rashi ne ga addinin Musulunci da kuma kasuwanci a yankin Afrika da ma duniya baki daya, ya ce za a dade ana tuna wannan baban rashi.

Ya kuma bayyana marigayin a matsayin shugaban Tijjaniya da ya yi zurfi cikin addini tare da samun wata kima ta musamman ga shi kuma mutun mai saukin kai wanda ya amfani rayuwar jama’a cikin da wajan kasar nan kuma ya rasu a matsayin wani jarumi.

Haka kuma gwamnan a madadin shi kan shi da jama’ar jihar Katsina suna mika sakon ta’aziyarsu zuwa ga Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi Na II da kuma shugabannin Darikar Tijjaniya tare da dansa Alhaji AbdulSamad Isyaku Rabi’u da sauran ‘yan uwa da iyalai da yin kira da ayi koyi da shi.

Daga karshe gwamna Aminu Bello Masari ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayi Khalifa Isyaku Rabi’u ya baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi da aka yi wanda ya ce rashi ne na kasa baki daya.


Advertisement
Click to comment

labarai