Connect with us

LABARAI

Buratai Ya Kaddamar Da Makon Horar Da Sojoji A Bauchi

Published

on


A jiya Talata ne, babban shugaban sojojin Nijeriya Laftanal Tukur Yusuf Buratai ya jagoranci kaddamar da makon horar da sojojin Nijeriya domin kara musu himma da kuma sanin dabarun yaki da kuma shawo kansa a kowani lokaci domin fuskatar dukkanin kalubalen tsaro a fadin kasar nan ta Nijeriya.

Taron makon horoswar, wanda suke gudanar da shi a kowace shekara, na bana ya gudana ne a jihar Bauchi inda aka yi sa a sabon muhallin shakatawa mallakin sojojin Nijeriya da ke Bauchi, makon horarsawar wanda suka masa suna da cewa ‘Combat Arms Training Week 2018’.

Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar, shugaban sojojin Nijeriya Laftanal Yusuf Tukur Buratai ya bayyana cewar yaki da ta’addanci aikinsu ne domin tsarkake Nijeriya daga kowace irin barazana, yana mai bayanin cewar shi wannan horon suna yi ne domin kyautata aikinsu na soji da kuma samar da sabbin dabarun yaki, kyautata aiki, da kuma kyautata fahimtar juna a tsakanin ma’aikatansu na bangarori daban-daban, hade kuma da kokarin tattauna yadda za a kawo karshen kowace irin matsalar tsaro da ke addabar Nijeriya.

Da yake bayani wa manema labaru jimkadan bayan kaddamar da makon horarsawa, Burutai ya ce, “Wannan taron muna gudanar da irinsa a kowace shekara domin sake zaburar da junanmu kan sabbin dabarun aiki domin horar da dakarunmu wajen inganta fannonin tsaro, kare kasa da kare jama’an kasar nan. don haka ne muka taru na musamman a yau (jiya kenan) domin bayar da horo wa jami’anmu na sojin kasa da kuma masu aiki a kan motoci masu sulge, a kowani lokaci wadanan sune a gaba-gaba wajen fuskantar yaki ko wani tashin-tashina, don haka ne kuma muka shirya musu horo domin horar da su kan daburun yaki don a inganta aikin soji a kowani lokaci,” A cewar Buratai.

Burutai ya bayyana cewar babban manufarsu kan irin wannan horarwar da suke baiwa jami’ansu na soji shine a kara basu darabun yaki da kuma sake gina kyakkyawar alakar aiki a tsakanin wadannan fannonin domin aikin soji yake tafiya daidai yadda ake so, kuma bisa salon zamani.

Da yake kira ga gwamnatocin johohin Nijeriya, shugaban sojojin Nijeriya, Yusuf Buratai ya bukaci gwamnonin da suke kokarin baiwa wa sojoji hadin kai da kuma dan alawus din ake nema daga garesu domin kwalliya ta ke biyan kudin sabulu wajen kyautata aikin soji a kowani lokaci.

Ta bakinsa, “Kirana gare gwamnonin jahohi su ci gaba da nuna mana wannan goyon baya da suke ba mu, musamman mun san cewar gwamnoni da yawa suna sanya kudade sosai, suna bamu motoci suna kuma samar mana da kayyakin aiki hade da biyan alawus-alawus na sojojin da suke aiki  a wuraresnu, don haka muna kira a garesu su daure su ci gaba da wannan domin mu ma mu samu karfin guiwa mu samu kwazon ci gaba da aikin tsaron kasa a kowani lokaci,” In ji Buratai.

Da yake tasa jawabin a wajen kaddamarwa, Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya fara ne da jinjina wa irin gudunmawa da kuma kokarin dakarun sojojin Nijeriya wajen kawar da ‘yan ta’adda da kuma masu neman kawo wa kasar ci ma baya.

M.A Abubakar ya bayyana cewar kokarin da sojojin suke yi wajen shawo kan matsalolin masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami da kuma uwa-uba matsalar mayakan Boko Haram da cewar abar a yaba musu ne gaya, ya bayyana cewar sojojin Nijeriya sun taka rawa sosai wajen wanzar da zaman lafiya a kasar nan musamman in aka yi la’akari da halin da Nijeriya ta samu kanta a shekarun baya.

Gwamnan Bauchi ya kuma nuna jinjinarsa wa shugaban sojojin Nijeriya Yusuf Buratai a bisa tsayuwar dakar da ke yi wajen kawo karshen ta’addanci a Nijeriya, hade kuma da samar da dabarun yaki wa dakarun sojojin Nijeriya domin kyautata musu aikinsu a kowani lokaci.

Da yake amsa tambayoyin manema labaru, jimkadan bayan kammala taron, gwamnan Bauchi ya bayyana cewar da bukatar gwamnoni suke dafa wa dakarun sojoji wajen yakar ta’addanci a kowani lokaci, yana mai shan alwashin ci gaba da taimakawa domin a samu gina kasa mai cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wakilinmu ya labarto cewar an zagaya da tawagar gwamnan, shugaban sojojin Nijeriya da wasu manya domin nuna musu irin makamai da kuma kayyakin yaki da sojojin Nijeriya suke amfani da su wajen yakar ta’addanci da kuma ci gaba da kare karar Nijeriya.

Kayyakin aikin da suka hada da bindigori, motoci masu sulken ungulu, alburusai da dai sauran manyan makaman da sojojin Nijeriya ke hadara da su wajen yakar masu ta’addanci, haka kuma kowace na’urar bindiga akan yi wa tawagar bayanin irin aikace-aikacenta dalla-dallah.


Advertisement
Click to comment

labarai