Connect with us

LABARAI

Za A Yi Zaman Makokin Mutuwar Dimokradiyya A Kaduna -Hunkuyi

Published

on


Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, Shugaban kwamitin hukumar Kidaya na kasa a majalisar Dattawa, wanda shi ne wakilin Majalisar Dattawa mai wakiltar kaduna ta Arewa, ya yi kira ga Al’ummar Jihar Kaduna, dama Nijeriya gaba daya, da su fara zaman makokin mutuwa da kuma birne dimokaradiyya a Jihar kaduna.

Sanatan ya fadi hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai a Kaduna, inda ya tabbatarwa manema labarai cewa basu ga ko mutum daya daga cikin wakilan jam’iyyar APC wanda aka daura masu alhakin gudanar da zaben Shugabancin jam’iyyar APC a mazabu 255 na Kananan hukumomi 23 dake fadin Jihar Kaduna ba, amma duk da hakan Gwamnatin Jihar har ta fitar da sanarwan cewa anyi zaben yadda ya kamata a dukkan fadin jihar.

Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin hukumar da take sanya ido akan yadda ake dauka da kuma rarraba mukamai na Gwamnatin Tarayya, ya yi kira da soke wannan sunaye da aka rubuta a matsayin anyi zabe.

Ya ce, “mutanen dake cikin gwamnati ako wani mataki ya kamata su kwana da sanin cewa mutane masu zabe su ne masu gona tare da manoma, domin haka bai kamata mutane su zama leburori ko kuma bayi ba a wannan gonar nasu ba.”

Sanatan, ya kuma yi gargadin cewa idan har Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Chif Oyegun, ya ci gaba da daukan irin wadannan muggan matakan, to tabbas zai iya jefa Jam’iyyar ta APC cikin duhu da rudani.

Hunkuyi ya ci gaba da bayyana cewa, “Da mu aka faro tafiyar Jam’iyyar APC, ba wai daukar mu akayi a kan hanya ba. Manbobinmu sun biya wasu kudi da ka’idojin jam’iyya ta kayyade cikin asusun Jam’iyyar APC, kuma muka karbi tela domin karban takardar tsayawa takaran mukamai da za ayi zabe akansu guda 9,453 a mazabu 255 dake kananan hukumomi 23 na jahar, Wanda ko wace hukumomi wanda ke da mukamai 37 daga kowace mazaba.”

“Manbobinmu suna shirye shiryen yin zabe kamar yadda aka tsara kawai sai mukaji gwamna yana gabatar da bayanai ga yan Jam’iyyar APC, inda har Shugaban Jam’iyyar APC na kasa yana wurin yake kalaman batanci wanda babu wani gwamnan a tarihin kasar nan da yataba yin haka, a inda har ya umurci mabiyansa da suci mana mutunci har da wanda ma ba dan jam’iyyarsa ba, wai domin kawai ra’ayinmu bai zo daya ba.”

Ya kara da bayyana cewa, “Kwamitin gudanar da zaben mukaman Jam’iyyar APC, sun bai wa kananan hukumomi guda biyu ne kacal fom din yin takara, daga cikin kananan hukumomi 23. Kuma ko wadanda aka bai wa fom din, an basu ne a daren ranar da za ayi zaben, misalin karfe 3:55 na safe, wanda shi ma ba haka dokar ta tsara ba, domin an ce duk wanda ya karbi fom din takara ya dawo da shi awa 24 kamin ranar zabe.”

“Domin haka wannan matakai da aka dauka yasa manbobinmu suka rasa yanda za suyi sai dai suje inda aka tsara yin zaben karfe takwas na safe, inda sukaje da telan da suka biya a bankuna da kuma katinsu na jam’iyyar APC domin su bada nasu gudunmuwar a zaben da za ayi. Amma abin da ya bamu mamaki shi ne, babu wani jami’in zaben da yazo daga cikin mazabu 255 tun daga karfe takwas na safe har yamma.”

Hunkuyi ya ce, “ Sakamakon da Gwamna Nasiru El-Rufai, ya fitar da sunan anyi zabe, an tsara shi ne daga Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, ba tare da an je kowaNe mazaba ba, daga cikin mazabun da muke da shi guda 255, kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar da umurnin ayi, amma ba ayi hakan ba, sannan ba abi dokar kundin tsarin mulkin kasa da na Jam’iyyar APC ba.”

Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, ya kara da bayyana cewa, “mun sami labarin cewa, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, bayan ya gana da Shugabannin mazabu da na kananan hukumomi a Gidan Gwamnatin Jihar kaduna, ya umurci Shugaban kwamitin gudanar da zabubbukan da aka shirya yi, Adamu Modibbo, da ya tabbatar ya mikawa Gwamna El-rufai, dukkanin tsare tsaren Jam’iyyar a hannunsa.”

Daga karshe, Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, ya yi addu’ar cewa, “Muna rokon Allah da ya kubutar da Jam’iyyar APC daga hannun makiyan dimokaradiyya, da masu daurewa zalunci da danniya gindi, ta hanyar ruguza Jam’iyyar APC.  Allah yaja zamanin Jam’iyyar APC, Shugaban kasa da kuma kasarmu Nijeriya baki daya.” A cewar Sanata Suleiman Othman Hunkuyi

 


Advertisement
Click to comment

labarai