Connect with us

LABARAI

Tasirin Jaridar ‘China Daily’ Ga Cigaban Kasar Sin

Published

on


Jaridar ‘China Daily’, ita ce jarida mafi girma da ake wallafawa a cikin harshen Ingilishi a duk fadin kasar Sin wadda aka kafa a shekarar 1981. Zuwa yanzu jaridar ta cika shekara 37 da kafuwa.

Ta kasance jaridar da aka fi wallafawa da yawa a tsakanin jaridun kasar Sin inda ake buga kimanin kwafe milyan daya da ake rarrabawa a sassan kasashen duniya. A Afirka kadai ana rarraba kwafenta kimanin dubu goma sha uku a kullu yaumin.

‘China Daily’ tana da manyan ofisoshi na rassa guda talatin da biyar a sassan kasar Sin, da kuma wasu goma sha takwas a wasu kasashen duniya. Kasancewarta jaridar da ta yi wa saura fintikau da adadin kwararrun masu aiko da rahotanni da uwa-uba nagartattun editoci masu tace labarai, ‘China Daily’ ita ce kan-gaba a duk yankin Asiya a tsakanin jaridun da ake wallafawa da harshen Ingilishi.

Jaridar ta samu damar fadada kafafen da ta ke yada labaru daga jarida ta takarda zuwa sauran manyan shafukan sadarwa na zamani kimanin goma. Wadanda suka hada da: babban shafinsu na intanet, manhajar waya, facebook, twitter, weibo, weChat da sauran kafofi. Bugu da kari, tana da reshe a shafukan intanet na wasu kafafen guda talatin sai kuma tashoshin musamman na intanet guda dari uku.

Da yake yi wa tawagar wakilin LEADERSHIP bayani a ziyarar da suka kai musu a shalkwatarsu da ke Birnin Beijing, Editan jaridun karshen mako na bangaren Turai da Afirka na jaridar ‘China Daily’, Mista Su Kiang ya bayyana cewa jaridar takan yi hadin gwiwa da kafafen yada labaran Afirka a duk lokacin da shugaban kasar Sin, Di Jinping yake ziyarar aiki a yankin. A cewarsa, a karkashin hadin gwiwar sukan yi musanyar labarai da hotuna domin amfanar da juna.

Ya kuma ce jaridar ta yi fice wajen wallafa labarai masu alfanu da kama hankalin makaranta, kana ya ce ko kwafe daya na jaridar ba ya kwantai a kasar Sin.

Dangane da yawan mutanen da ke karanta jaridar ta shafukan intanet kuwa, Mista Su Kiang ya ce suna da mabiya a kafofin sada zumunta na intanet sama da milyan dari (100,000,000).

Har ila yau, wani abu da Editan ya ce ya kara wa jaridar tagomashi shi ne bullo da shafuka na musamman da suka mayar da hankali kan wallafa rahotanni masu janhankali da suka dace da wannan zamanin. Musamman akwai sashen da ke kara wa maso koyon harshen Ingilishi gogewa a cikin jaridar, sannan a karkashinta sukan hada gasa a tsakanin Sinawa masu magana da Ingilishin.

Editan ya ce jajircewar da jaridar China Daily ta yi a kan aiki, ta ba ta damar samun lambobin yabo daban-daban. Na baya-bayan nan shi ne lambar yabon da aka ba ta a kan iya tsara shafin jarida. A cewarsa, suna tura masu daukan hoto zuwa kasashe daban-daban su dauko hotunan muhimman wurare masu kayatarwa domin wallafawa a jaridar. Ya kara da cewa a yankin Asiya kadai, suna da masu karanta jaridar sama da mutum milyan hamsin.

An tambayi Mista Kiang ko akwai ‘yan kasashen waje da ke aiki a ‘China Daily’ ganin cewa jaridar mallakar gwamnati ce watakila ‘yan kasa kawai ake dauka aiki? Ya ba da amsa da cewa, “Muna da ma’aikata guda dari daga kasashen waje daban-daban da ke magana da harshen Ingilishi. Ma’aikatan da muke da su a bangaren yada labarai sun kai mutum dari hudu zuwa dari biyar, amma idan aka hada da ma’aikatan sauran sassa, wato irin su sashen tallace-tallace, kudi da gudanar da mulki da sauran su, ma’aikatanmu sun haura sama da dubu daya”.

Editan ya kuma nunar da cewa a yini daya jaridar tana iya samun kudin shiga RMB (kudin kasar Sin) milyan daya, sannan gwamnatin kasar tana ba su tallafi a koyaushe inda hakan ke matukar taimaka wa ayyukansu na yau da kullum.

Bisa al’ada, duk wani gidan jarida yana da lokacin da ake kayyadewa na kammala aiki domin samun rarraba jaridar da aka wallafa a kan kari, Mista Kiang ya ce sukan kammala komai da komai jaridar ta fito da dim-diminta da misalin karfe goma sha biyu na dare.

Domin karfafa zumuncin aiki, Jaridar ‘China Daily’ ta ce ta yi gamayya ta fuskar sadarwa, kwantiragi da horaswa da sauran sassa masu alfanu. Sannan akwai kawance tsakaninta da manyan kafofin yada labaru na duniya da suka hada ‘Reuters’, ‘The Associated Press’, ‘Agence France-Presse’, ‘The World Street Journal’, ‘The Washington Post’, ‘Bloomberg da kuma ‘BBC’.

Ta fuskar karfafa difilomasiyya da sadarwa a cikin gida da waje kuwa, jaridar ta shirya manyan tarurruka na duniya da suka hada da taron tattaunawa kan shugabanci na yankin Asiya, gasar hotunan jaridu na yankin Asiya, taron horas da matasan ‘yanjarida, gasa a tsakanin masu magana da harshen Ingilishi a karne na 21 ta kasar Sin, taro a kan yadda kasar Sin ta ke a idanun kafofin yada labarai na waje. Akwai kuma gasar da China Daily ta kaddamar a shekarar 2006 ta bidiyon mutum-mutumi (cartoon) game da kare lafiyar muhalli. Gasa ce da ake fafatawa a tsakanin daliban kwalejin fasaha daga sassan duniya. A cewar wata takardar bayani game da ‘China Daily’, wadannan tarurrukan sun karfafa sadarwa ta bangaren masana’antu, ilimi da harkokin kasuwanci sannan uwa-uba manyan hukumomin duniya sun na’am da su.

Bayan haka, a shekarun 2016 da 2017, jaridar China Daily ta shafin intanet (Chinadaily.com.cn) ta shirya wani taron hadin gwiwa na kafafen yada labarun kasar Sin da na kasar Rasha wanda aka yi lakabin “Taron kafafen yada labarun kasar Sin da na kasar Rasha na shekara”. Taron shi ne mafi girman fagen da aka tattauna batun shafin intanet a tarihin kasashen biyu.

Bugu da kari, akan gayyaci ‘yanjarida na kasashen waje; galibi wadanda suke mambobin Kungiyar ‘Yanjarida na Yankin Asiya, zuwa kasar Sin domin gane wa idonsu irin cigaban da kasar Sin ke samu a wannan zamanin ta fuskar tattalin arziki, siyasa, al’ada da kuma yawon bude ido. Ko shakka babu, wannan ya kara wa kasar kima a kasashen waje.

Irin rawar da jaridar China Daily ke takawa wajen sadarwa a tsakanin masu mulki da al’ummar da ake mulka ta kasar Sin ba za ta misaltu ba, ganin cewa hakan na matukar yin tasiri ga bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin Sinawa.


Advertisement
Click to comment

labarai