Connect with us

LABARAI

Shugabannin APC Ba ’Yan Amshin Shata Ba Ne -Audi

Published

on


Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

An kira ga ‘yan jam’iyyar APC da su kara dunke wa waje daya domin kar su baiwa ‘yan adawa damar sanin wainar da suke toyawa. Malam Audu Ibrahim wani jigo a jam’iyyar ne ya yi kiran a lokacin da yake mayar da martani kan masu adawa da jam’iyyar.

Ya ce mu a jam’iyyar APC ba wani shugaba tun daga matakin mazaba har zuwa jiha da yake dan amshin shata, manufar guda kuma akan ta muke tafiya. ‘Yan adawa ne ke kirkiro labarai marasa kan gado suke yarfawa ga APC.

Dangane da maganar tsayar da ‘yan takara kuwa, Malam Audu yace iya saninsa jam’iyyar APC, jam’iyya ce mai adalci duk dan takarar da jama’a suka amince da shi lallai shi dan takarar jam’iyya. Masu maganar kowa ya iya allonsa ya wanke wani ma bai kusa za a wanke mai kuma ayi nasara, bai yiwu wa an yi shekaru sha shida ana kwamacala sannan dare daya cikin shekaru uku kawai a ce abubuwa sun daidaita, abin ai ba saddabaru ba ne. Ina jawo hankalin jama’a da

su kara hakuri canjin nan da ake magana fa kowa shaida ne an fara ganin shi ai.

Ina mai jawo hankalin masu sha’awar yin takara a 2019 da su tabbatar sun yi abubuwan da zasu kai jam’iyya ga nasara, ba wai tunanin cin zabe ko ta wani hali ba, shi lamarin takara yana dauke da abu biyu kuma dole kayi imani da shi, nasara da akasinsa, idan muka rungumi wannan tabbas APC za ta ci gaba da samun galaba a dukkanin zabuka masu zuwa.

Maganar wai da ake cewa duk dan takarar da ya zo jam’iyya ana yi mai alkawalin mara mar baya, to ka taba ganin inda uwa za ta ki ‘yayanta, duk za na kwarai dole ya nemi albarkar Iyaye kuma a matsayin jam’iyya ai ba za ta ki karban ‘yayanta ba. Abin da na ke kara jaddadawa shi ne ya zama wajibi ga duk mai son ci gaban jam’iyyar nan ya zage damtse wajen samar da jam’iyya za ta ci gaba.

Ina tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewar nasarorin da suke gani an samu yanzu musamman farfado da harkar noma, tattalin arziki da hanyoyin da ake na lalubo yadda za a magance matsalar tsaro bai rasa nasaba da hadin kai da addu’o’in da ‘yan Nijeriya.

Yadda ‘yan Nijeriya suka bada hadin kai wajen samar da nagartattun ‘yan takara a zabukan 2015 haka zamu sake zage damtse wajen ganin 2019 mun ci gaba da inda muka tsaya, saboda haka manufar APC ita kyautatawa tare da inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai