Connect with us

LABARAI

Samar Da Kayan Aikin  Zamani Zai Taimakawa Noma A Kasar Nan -Danmari

Published

on


Anyi kira ga Gwamnatocin jahohi a kasar nan da cewa yakamata su sake tsari wajen tallafawa ci gaban noma ta koyi da yanda wasu kasashe suke,wanda ba kudi suke bayar wa ba illa suna samar da kayan aikin gona ne ga manoman a inda suke noma.

Shugaban Kamfanin harkar kayan noma na “Kaigama agricultural machinary” Alhaji Usaini Usman Danmari ya bayyana haka a Kano.

Yayi nuni da cewa a wasu kasashe ana yin “lands keeping” ne da kamfani ke kawo duk abin da manomi ke bukata kusa da shi a ba shi akan bashi sai ya noma ya rika maida kudi ta ka’idar da aka yi.

Ya ce yanzu haka Gwamnatin jahar Sakkwato ta soma yunkurin yin hakan tareda mutanen Chana, za a zo a gyara wajene kamar hekta a yi sito a gona a ajiye duk kayanda manomi zai nema na aikin, su manoma za su yi kungiya da shugabanninsu za a rika basu kaya a inda aka tanada na amfani da za ayi dashi in suka noma su rika biya a hankali wannan Gwamnatin Sakkwato na shirin somawa.

Ya ce idan aka samar da irin wannan tsarin a jahar kano zai taimaka ga kokarin Gwamnati,a matsayinsu na masu kayan aikin gona za su hada kai da gwamnati dan yi wannan tsarin na “landskeeping”.

Alhaji Usaini Usman Danmari yayi nuni da cewa harkar noma sai Gwamnati tasa hannu misali a  tsarin manomi za a bashi za a bashi kayan N10,000 ya biya N2,500,sauran N7,500 daga tallafin Gwamnati zai fito kuma sannan ga manomi N2,500 ba’a lokaci guda zai biya ba a hankali ta hanyar abin da ya noma wannan zaisa a sami ci gaba.

Shugaban Kamfanin”Kaigama Agricultural Machinaries” Alhaji Usaini Usman yayi nuni da cewa noma a gida yafi shigo da abinci daga waje in aka tsaya aka kyautata noman sai dai ma a fitar daga kasar nan akai wasu kasashen  dan akwai kasar noma ko’ina a kasar nan ba karama ba.

Ya ce akwai wani tsari nayin rijiyoyi maimakon dam da za a hada mutane kamar 10 zuwa 20 a basu rijiya daya ita zata basu ruwa da za su rika noma in akayi haka za a sami ci gaba sosai.

Ya ce idan mutane za su tsaya su taimaki kansu duk kayan noma da aka basu karsu sayar su tsaya su koyi aiki dashi dan yawanci zakaga idan aka basu sayarwa suke.

Abu ne mai sauki ga manoma su daure wajen koyon yanda ake sarrafa irin wadannan injuna na noma na zamani hakan zai taimake su sosai wajen bunkasa ci gaban harkokin noma.

 


Advertisement
Click to comment

labarai