Connect with us

LABARAI

Munanan Ayyukan Da Ake Aikatawa, Duk Don A Rage Wa Buhari Kima Ne –Sarkin Katsina

Published

on


Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya yi zargin cewa, duk munanan ayyukan da kashe-kashen da ake ta yi a wasu sassan kasarnan, duk ana yin su ne da nufin bata wa Shugaba Buhari suna, da kuma bata shaksiyarsa.

Basaraken ya bayyana hakan ne a fadar sa ranar Litinin sa’ilin da Shugaba Buhari, ya kai wa Masarautar ta Katsina da iyalan babban Limamin Katsina, Muhammadu Liman Lawal, 92, ziyarar ta’aziyya.

Ya shaida wa Buhari cewa, masu neman ganin bayan sa ba za su taba cin nasara ba, duk da farfagandar karyar da suke ta yadawa a kafafen labarai, domin ainihin ‘yan Nijeriya su na nan a tare da shi.

Ya ce, wahalar da ake sha a Shugabancin Nijeriya ya danganta ne da kasantuwar kashi 80 na matsalolin Nijeriya duk mutane ne suka kirkire su.

Daga nan sai ya nemi Shugaba Buhari da ka da ya gajiya a kokarin da yake na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, sannan kuma ya yabi Gwamna Aminu Masari na Jihar ta Katsina wanda ya siffanta da sarkin aiki da kuma kokarin inganta rayuwar al’ummar ta Jihar Katsina.

Ya bayar da tabbacin, duk Shugaban da yake jagoranci tare da sanya tsoron Allah, tabbas zai yi nasara.

Dangane da tsohon Liman din, Basaraken na Katsina, ya yaba masa matuka, ya kwatanta shi da babban malami mai hakuri waliyin Allah, wanda ya yi wa al’ummar Katsina da Musulmai hidima ta tsawon shekaru 40.

Tun da farko a na shi jawabin, Shugaba Buhari, ya yi rokon gafarar Allah ne ga mamacin, tare da fatan Allah ya baiwa zuriyar sa jimirin daukan rashin na shi.

Shugaba Buhari, ya yi hutun sa na karshen mako ne a mahaifar sa ta Daura, ya kuma halarci zabukan mazabu na Jam’iyyar APC da aka gudanar a duk kasa a mazabar Sarkin Yara ‘A’ a garin na Daura, Gwamna Masari, ne ya yi masa bankwana tare da manyan jami’an gwamnatin sa, sa’lin da ya tashi daga Filin Jiragen sama na Umaru Musa ‘Yar’aduwa

 


Advertisement
Click to comment

labarai