Connect with us

LABARAI

Kisan Gillar Birnin Gwari: El-rufai Ya Fashe Da Kuka 

Published

on


Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ya katse ziyar rangadin Kananan Hukumomin da yake yi domin mikawa  ‘yan takarar Shugabancin Kananan Hukumomi karkashin inuwar jam’iyyar APC, tutar domin wakiltar jam’iyyar APC a zaben Kananan Hukumomi dake tafe ranar Asabar, 12 ga watan Mayu, idan Allah ya kaimu.

Gwamnan wanda ya isa Birnin Gwarin tare da tawagar manyan kusoshin jami’an Gwamnatin Jihar kaduna, sun fara da Kai ziyarar ta’aziya Fadar Mai Martaba Sarkin Burin Gwari, Alhaji Zubairu Mai Gwari Na II.

A yayin da yake jawabi, Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ya ce, “Mai Martaba Sarki, yau na yanke duk wani abu da nake yi ne don in kawo maka wannan ziyara  domin  in jajanta wa al’ummmar masarautar Birnin Gwari, na wannan masifa da ya faru a Gwaska inda wasu ‘yan ta’adda kuma makiyanmu suka kashe ‘yan’uwanmu ba  tare da wani dalili ba.”

Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa, “Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, kuma ya ba mu hakurin rashi na ‘yan’uwanmu da muka rasa. Allah ya kawo mana karshen wannan masifa kuma ina ba ku tabbacin cewa, Gwamnatin Tarayya, ta amince za ta kafa rundunar sojoji da na ‘yan-sanda a wannan yanki na Birnin Gwari. Tun da muka zo gwamnati, ba abin da muka fi ba fifiko irin tsaro.  Ba abin da ke hana ni sukuni, in kasa barci irin in ji an rasa rai a Jihar Kaduna domin  na tabbatar Allah zai tambaye ni.”

Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ya kara da bayyana cewa,  “Wannan masifa da ta same mu na rasa rayukan ‘yan’uwanmu da aka yi , ya sa na hakura da zagayen da nake yi Kananan hukumomi don yakin neman zabe da na fara jiya saboda in zo in jajanta muku, kuma in kara tabbatar muku da irin kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna, ke yi na ganin mun tsare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu.”

“Ina mai tabbatar muku, Insha Allahu yadda muka yi kokari na ganin an samu tsaro a Kudancin Jihar Kaduna, Birnin Gwari ma da sauran wuraren da muke fama da matsalar tsaro zai kawo karshe.

Mai martaba Sarki, yanzu haka daga nan zan je Gwaska inda aka kashe wadannan mutane don mu gane wa kanmu irin barnar da aka yi masu, domin mu san matakin da za mu dauka, kuma duniya ta ga irin barnar da ake yi a wadannan yankuna na Birnin Gwari da Zamfara, domin jaridunmu ba su daukar  irin wadannan Labaran.” A cewar Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, a yayin da yake jawabi a Fadar Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari.

Daga bisani gwamnan ya ziyarci Garin na Gwaska, inda ya gane ma idonsa yadda ‘yan ta’adan suka sami nasarar mutane mutane masu dimbin yawa, sannan daga bisani suka cinna ma garin wuta. A lokacin ziyarar, Gwamnan Jihar kaduna, ya fashe da kuka sa’ilin da ya ci karo da alburushin harshahen manyan bindigogi masu sarrafa kansu da ‘yan ta’addan suka yi amfani da su wajen hallaka daukacin mutanen garin.

Gwama El-rufai wanda a cikin kuka da nuna alhininsa, ya karantawa mutanen Gwaska, sannan ya basu tabbacin cewa nan ba jimawa ba, jami’an tsaro zasu kamo duk wasu masu hannu a cikin wannan lamari, domin hukunta su.


Advertisement
Click to comment

labarai