Connect with us

LABARAI

Khalifa Isyaka Rabi’u Ya Rasu

Published

on


Daga Sulaiman Bala Idris

A jiya ne Allah ya yiwa Khalifa Isyaka Rasuwa yana dan shekaru 90 a duniya.

Marigayin ya kasance daya daga cikin mashahuran Malamai, kuma babban dan Kasuwawanda ya shahara a tsakankanin 1970s da 1980s.

Kafin rasuwarsa, Khalifa Isyaka Rabiu ya kasance daya daga cikin jagororin Darikar Tijjaniya a Nijeriya.

Iyalan Marigayin ne suka sanar da rasuwarsa jiya, inda suka bayyana cewa ya rasu ne a wani asibiti dake Birnin Landan.

Khalifa Isyaka ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya da dama, wanda a cikin ‘ya’yan nasa akwai Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu.

An haifi Khalifa Isyaka Rabiu a gidan Malam Muhammadu Rabiu Dan Tinki, wani shahararren masanin Al-kur’ani a garin Bichi ta Jihar Kano. Sannan kuma a marigayin yayi karatun addini; Al-kur’ani da larabci a makarantar mahaifinsa daga shekarar 1936 zuwa 1942. Sannan kuma marigayin ya je garin Maiduguri na Jihar Borno inda ya karo ilimin addini.

A farkon 1950 lokacin Khalifa Isyaka Rabiu na koyarwa, sai kuma ya hada da kasuwanci, inda ya assasa  ‘Isyaka Rabiu & Sons’ a shekarar 1952.

 


Advertisement
Click to comment

labarai