Connect with us

LABARAI

Kalaman Batanci: Sarkin Musulmi Ya Yi Wa ’Yan Siyasar Kaduna Nasiha

Published

on


Daga Sulaiman Bala Idris

A jiya ne Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar ya gargadi ‘yan siyasa dangane da irin kalaman batancin da suke amfani da shi, musamman ma bisa la’akari da yadda zaben shekarar 2019 ke karatowa.

Sarkin na Musulmi ya yi wannan kira ne musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna da ‘yan siyasar Jihar, sakamakon kalamai marasa dadi da suke jifan juna da su.

Idan dai ba a manta ba, tun ranar 29 ga watan Maris Gwamna el-Rufai suka fara ‘yar tsama da Sanatoci uku na Kaduna, sakamakon kin amincewa da ba gwamnan damar cin bashi daga bankin duniya. A dalilin haka ne Gwamnan ya yi ta la’antar sanatocin, karshe ma har da fadin ba su da asali.

Sarkin Musulmi yayi wannan nasiha ne a lokacin da yake gabatar da lakcar maraba da azumin Ramadan, wanda Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta shirya a Kaduna. Sultan ya nuna damuwarsa dangane da abin da ke faruwa tsakanin gwamnan da sauran ‘yan siyasan.

Sarkin ya yi kira ga ‘yan siyasan da su mayar da wukaken, su bi a hankali wurin amfani da kalamai, domin Kaduna ce zuciyar arewacin Nijeriya.


Advertisement
Click to comment

labarai