Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Ayyana Sunayen Masu Kamfanoni

Published

on


Daga Bello Hamza

Sakataren gwamnatin tarayya Mista Boss Gida Mustapha, ya ce, a halin yanzu gwamnatin tarayya ta shirya tsaf kuma nan gaba zata bayyana wa jama’a sunayen mutanen dake da kanfanoni da manyan kaddarori a kasar.

Mista Mustapha ya bayyana haka ne ranar Litinin a yayin bukin bude taron “Open Gobernment Partnership week”, hakan zai saukaka bincike a kan mutane dake fuskanta tuhumar daya shafi mallakar kanfanoni a kasar nan.

‘’A karon farko a Nijeriya sirranta amsu malakar kanfanoni a kasar nan zai zama tarihi a lokacin da za a fara amfani da kundin dake dauke da sunayen ‘yan Nijeriya dake da hannu a kanfanonin dake a sassan kasar nan.

‘’Gwanati ta kuma samu tabbaci daga hukumar ragistan kanfanoni na kasa “Corporate Affairs Commission (CAC)” cewar, a nan gaba zata rinka bayar da sunayen mutanen da suka da kaso mafi tsoka a kanfanoni da zaran an bukacin haka.

‘’Tare da wadannan matakai namu, ina da kwarin gwiwar cewar, binciken badakalar da suka hada da lamarin mallakar kanfanoni a kasar zai yi matukar sauki” inji shi.

Ya wara da cewa, a ciki mako uku masu zuwa, ofishin sakataren gwamnatin tarayya zai sabunta shafinsa na intanet mai suna OSGF.GOB.NG da Eparticipation.gob.ng domin amfanar ‘yan Nijeriya, za a kuma hada wannna shafin da dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati, ta haka za a iya gabatar da koke kai tsaye daga ma’aikatun gwamnatu zuwa ofishin sakataren gwamnatun tarayya.

Ya ce, fiye da kowanne lokaci a tarihin kasar nan, gwamnatin tarayya na cikkaken yaki da cin hanci da rashewa, ana kuma samar da tsarin tattalin arzikin da zai tallafa wa dukkan dan Nijeriya, ana kuma samar da tsarin maganin sake aukuwar satar da aka tafka a shekarun baya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai