Connect with us

LABARAI

Garkuwa Ta Karrama Gwaraza Tare Da Tallafi Ga Marasa Karfi

Published

on


An bayyana cewar lokaci ya yi da masu hali da ma’aikatan gwamnati zasu rika taimakawa al’umma, yanayin da muke ciki a yau abin yafi karfin gwamnati ya kamata ya bada na shi gudunmawa wajen cigaban kasa da al’umma.

Shugaban gidauniyar Garkuwan Talban Minna Foundation, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida ne ya bayyana hakan a lokacin da yake bayani ga dubban jama’ar da suka taru dan shaidar karrama wasu muhimman mutane da suka taka rawar ganin cigaban kasa da al’umma su dari biyu da kuma tallafi kudi ga kungiyoyi masu zaman kansu da daidaikun jama’a marasa karfi da aka yi a babban dakin taro na tunawa da mai shari’a Legbo Kutigi da ke minna.

Garkuwan Talba ya cigaba da cewar maganar gaskiya ya kamata gwamnati da duk wani mai abin hannun sa da a samar da hanyoyin da za a rika tallafawa jama’a dan saukaka masu halin kunci da suke ciki na tashi da tsadar rayuwa, yau idan ma’aikacin da ke amsar albashin naira dubu ashirin zai iya ware naira dubu biyar dan taimakawa koda a makocinsa ne kawai za ka iske jama’a na samun walwala kuma tausayi da mutuntawa zai dawo a zamantakewar al’umma.

Magabatan da suka shude ba wai sun tara abin duniya ba ne ko sun gina manyan gidaje yasa yanzu ke girma ma su ba, illa tausayi da taimakekeniya da suke gudanar wa a tsakanin al’umma shi ya jawo martabar da suke samu a yanzu.

Duk dan Arewa ya ga irin namijin aiki da marigayi sardaunan sokoto ya gudanar a kasar nan da yasa yanzu wasu ke kokarin lakabta sunayensu da shi, idan ka za gaya kasar ba ka ganin wani kasaitaccen gida ko kamfani da sunan sardauna ko tafawa balewa, shi me zai hana mu dawo akan irin wannan akidar.

Manufar shirya wannan taro shi ne zakulo mutane da suka ta ka rawa wajen kawo cigaban kasa. Yau mun karrama mutane dari biyu da lambar yabo, kamar irin su Ali Sarkin Mota, direban sardauna da Sani Malami jami’in tsaron sardaunan, taro ya gayyato irin su Malam Nigga na kaduna wanda ke da cibiyar horar da yaran da suka samu Kansu a shaye-shaye da ma kungiyoyin addini da na ‘yan kasuwa. Wannan mun yi ne kara masu azama da nuna godiya akan bajintar da suka nuna wajen cigaban kasa.

Da yake karin haske, shugaban taron, tsohon ministan wasanni, Malam Muhammadu Sani Ndanusa, yace wannan taron abin a yana ne domin taro ne tunatar da jama’a muhimmancin jajirwa da taimakon jama’a.

Wani babban al’amari da jama’a su ka yi watsi da shi, shi ne taimako, taimakon nan ya kunshi samar da kayan more rayuwa ga jama’a ga wadanda Allah ya baiwa arziki, taimakawa marasa karfi ta fuskar ilimi da kiwon lafiya.

Har ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa na da rawar takawa wajen bada tallafi, idan mun kwatanta da shugaban wannan gidauniyar, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida wanda dan kasuwa ne wani mai karfin arziki ba ne amma yana karfin imani dan yana zuciya mai kyau, da jama’a zamu dauki irin wannan turbar da mun samar da cigaba sosai a cikin al’umma.

Da yake tattaunawa da wakilin mu daya daga cikin wadanda aka karraman, Mustapha Nasiru Batsari wakilin muryar amurka. Yace wannan karamcin ba shi aka yiwa ba kusan ya shafi dukkanin abokan aikinsa, wannan na nuna duk irin abinda mutum yake yi jama’a na kallonsa, dan haka ina mai jan hankalin ‘yan uwana abokan aiki da mu kara jajircewa mu sani wannan aikin ba kawunan mu muke wa aikin ba, kasar mu ce muke yiwa hidima kuma yace a mudadin ‘yan jarida ‘yan uwansa suna godiya bisa wannan karamcin da akai masu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron dai akwai gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, sai tsohon ministan wasanni, Malam Muhammad Sani Ndanusa, sai tsohon babban jojin jiha, mai shari’a Jibrin Ndajiwo da sarakunan gargajiya, Malam an addini da shugabannin kungiyoyi.


Advertisement
Click to comment

labarai