Connect with us

LABARAI

Birnin Gwari: Kokarin Da Muke Yi Na Kawo Karshen Rigingimun Kaduna, Benuwe Da Taraba –Buhari

Published

on


Shugaba Muhammadu Buhari, ya amince da kafa wata sabuwar rundunar Soji, da kuma sabuwar rundunar ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Gwari, ta Jihar Kaduna.

Amincewar na shi yana daga cikin matakan kara tsaro don fuskantar ayyukan ta’addanci a wannan sashen, Kakakin Shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin da yamma.

LEADERSHIP A YAU, ta kawo maku rahoton kisan da aka yi wa wasu gomomin mutane ranar Asabar a wani harin da aka kai a garuruwan na Birnin Gwari.

Sarkin na Birnin Gwari, ya fada a ranar Litinin cewa, yawan mutanan da aka kashe ya haura zuwa 58.

Hatta Sojoji da ‘yan sanda an kashe a wasu hare-haren na ‘yan ta’addan a baya a karamar hukumar.

Shugaba Buhari, ya yi Tir da kashe ‘yan Nijeriyan da ba su ji ba, ba su gani ba, in ji Shehu.

“Na damu matuka da wannan kashe-kashen na rashin Imani da ‘yan ta’addan ke yi. Ina jin kunar hakan, ina kuma taya iyalan mamatan jimami, wannan gwamnatin za ta yi duk abin da take iyawa ta tabbatar ta murkushe wadannan makiya al’umman,” in ji Shugaba Buhari.

Garba Shehu ya ce, wannan sabuwar rundunar da za a kafa ta Soji da ‘Yan sanda ita ce ta baya-bayan nan wajen abubuwan da ake yi na karfafa samar da tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi, a ciki da sassan Jihohin Benuwe, Kaduna, Taraba, Zamfara da Nasarawa.

A satin da ya gabata ne, rundunar Sojin sama ta karbi wasu sabbin Jiragen Helikwafta na yaki guda biyu, a wani yunkuri na yakar ta’addanci a kasarnan.

Ta kuma kafa wata cibiyar bayar da agajin gaggawa a Jihar Taraba, sa’ilin da aka kafa runduna ta musamman ta shiga Tsakani a Jihar Benuwe, in ji Shehu Garba.

Sai dai kuma, duk da samar da wadannan rundunonin, an ci gaba da kashe-kashen fararen hula a Jihohin na Benuwe da Taraba.

“Wadannan kashe-kashen da suka ki ci, suka ki cinyewa, akwai wasu batagari da suke cinna su a boye da nufin aukar da yaki a kasarnan, domin wata manufa ta kashin kansu,” in ji Shugaba Buhari, a cikin sanarwar.

Buhari, ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan mamatan na kwana-kwanan nan, da kuma gwamnati da al’ummar Jihar Kaduna kan wannan babban abin takaicin da ya auku. Ya kuma yi alkawarin gwamnatin sa ba za ta taba yin watsi da su ba.


Advertisement
Click to comment

labarai