Connect with us

LABARAI

Bill Gates Ya Yi Hasashen Wata Cuta Da Za Ta Kashe Mutum Milyan 30 A Wata Shida

Published

on


Wata cuta da ake tsammanin tana tunkarar duniyar nan, wacce za ta zama babbar annoba, kamar yadda sanannen attajirin nan na duniya, Billa Gate, ya labarata a wani shirin talabijin mai suna ‘Annoba,’na ranar Juma’a.

Ba mu shirya mata ba.

Wata cutar mura ce mai kama da bala’in influenza, za ta iya kashe mutane milyan 30 a cikin watanni 6 kacal, Bill Gates ya ce, cutar ta gaba ba tilas ce ta kasance mai kama da mura ba, za ta iya kasancewa wata aba ce da sam ba a san ta ba a duniyar nan.

Ya kamata a shirya mata tamkar yadda ake shirya wa zuwan yaki, in ji Bill Gates.

In akwai abin da ya kamata mu sani a tarihi, shi ne wata cuta mai hadarin gaske da za ta addabi duniya bakidaya.

Hakan zai iya faruwa ma kila nan da shekaru goma ma su zuwa. Sannan kuma ga shi sam ba mu shirya mata ba.

Kamar yadda Bill Gate, din ya ce, a kullum shi mai yawan hasashe ne, ya tuna wa mutane cewa, muna fitar da kananan yara daga kangin talauci a duk duniya, muna kuma yin kokarin kawar da cutuka kamar na Polio da cutar Maleriya.

Amma, “Akwai wani sashen da sam duniya ba ta damu da yin komai a kansa ba,” in ji Gate. Shi ne kuwa bala’in da ke tafe.

A kullum yiwuwar faruwan hakan kara karuwa yake yi. Wannan sabuwar cutar tana iya zuwa kowane lokaci sakamakon kara yawan da duniya ke yi, mutane kuma su na kara taruwa a waje guda. Ya na da sauki sosai, mutane su kirkiri wata cutar da za ta iya yaduwa tamkar wutar daji a duk duniyar nan.

Sakamakon wani bincike da cibiyar, Institute for Disease Modeling, ta gudanar, wanda Bill Gate ya gabatar, wata sabuwar cuta mai kama da mura wacce ta kashe sama da mutane milyan 50 a shekarar 1918, akwai yiwuwar wannan za ta iya kashe mutane milyan 30 a cikin watanni 6 yanzun haka. Wannan cuta kuma da ke tunkarar mu nan gaba kadan, zai yiwu wannan ne karo na farko da za mu ganta a duniyar nan, in ta bullo, kamar da abin da ya faru na kwanakin baya kan cutar, SARS da MERS.

Idan da za ka shaidawa gwamnatocin duniyar nan cewa ana nan a na kera wasu makaman da za su iya kashe mutane milyan 30 don haka akwai bukatar a yi azaman magance lamarin.

Lokacin da Soji suka shirya yakar cutar ‘yan rani, sakamakon shi ne, cutar ‘yan rani 1 Mutane kuma sifili,” a cewar Bill Gates.

A wata hanyar kuma cewa yake yi, ya kamata mu shirya tarbar wannan cutar a yanzun kamar yadda muka shirya wa sauran cutukan na baya. Muna da kwayoyin da akalla za su iya rage kaifin cutar. Da kuma magungunan ‘antibiotic’ da za su iya yin na su kokarin da sauran su.

Ya kuma bayyana cewa, cibiyoyin bayar da gudummawa na, Bill Gates da kuma na Milinda Gates za su bayar da gudummawar dala milyan 12 domin karfafa samar da wadannan alluran.

 


Advertisement
Click to comment

labarai