Connect with us

SIYASA

Yadda Zaben Shugabannin Gundumomi Na APC Ya Gudana A Adamawa

Published

on


A jiya lahadi ne jam’iyyar APC ta gudanar da zaben sabbin shugabanninta a matakin unguwanni a jihar Adamawa, zaben da ya gudana lami-lafiya in banda matsalolin rashin isowar malaman zabe kan kari a wasu muzabu.

Rahotannin dake fitowa daga daukacin sassan kananan hukumomin jihar 21, na nuni da yadda zaben ya gudana lafiya a wurare da dama, to sai wasu ya’yan jam’iyyar sun koka da cewa basu samu daman kada nasu kuri’ar ba.

Shi ma dai kakakin majalisar dokokin jihar Honarabul Kabiru Mijinyawa, yace abun farin ciki ne yadda zaben ya gudana lafiya a jihar.

Yace “na yi farin cikin ganin yadda zaben unguwannin ya gudana lafiya ba tare da samun wata matsala ba, wannan abun farin ciki ne, da ke nuni da hadinkan ya’yan jam’iyyar a jihar” inji Kabiru.

Da yake magana game da koke-koken da wasu ya’yan jam’iyyar ke yi kuwa Kakakin majalisar yace “ dama zabe ba’arabashi da haka, haka shine dimokradiyya, kuma kasan kowa na da ‘yancin fadin albinda yakeso”.

Masu kada kuri’a a mazabar Wuro-Hausa, dake karamar hukumar Yola ta arewa sun koka da cewa ba’ayi zabe a mazabar ba, sukace sun dauki lokaci mai tsawo suna jira ba tare da malaman zaben sun ido ba.

“kaga mun dauki lokaci mai tsawo muna jira, amma har yanzu malaman zaben basu iso nan mazabar ba” inji jama’ar.

Da yake magana game da yadda aikin zaben ke gudana kuwa shugaban kwamitin gudanar da zaben Musa Mahmoud, yace wurare da dama da suka ziyarta zaben ya gudana yadda ya dace, ba kamar yadda aka zata da farko ba.

“bamu tsammaci zaben zai gudana haka ba, yadda ya’yi zafi bamu dauka ayi a gama lami-lafiya haka ba, muna yiwa Allah godiya” inji Mahmoud.

Da yake magana game da koke-koken rashin isowar makaman zabe akan lokaci kuwa shugaban kwamitin zaben yace “babu mazabar da ba za’ayi zabennan, duk inda aka samu jinkiri zamu tabbatar an magance matsalar” injishi.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai