Connect with us

LABARAI

Satar Sandar Majalisa: Majalisar Dattawa Ta Bukaci ’Yan Sanda Su Gurfanar Da Wadanda Suka Kama

Published

on


Majalisar Dattijai ta Bukaci Shugaban ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, da ya yi umurni da a hanazarta gurfanar da mutane shidan  da suka kama da aikata laifin aukawa zauren Majalisar suka sace Sandar Majalisar a watan da ya gabata.

‘Yan bangan da ake zargin, sun auka zauran majalisar ne a ranar 18 ga watan Afrilu 2018, daidai lokacin da Majalisar ke gabatar da zamanta, suka kuma sace sandar ikon majalisar da karfin tsiya.

Hotunan dai mutanan da ake zargin da ‘yan sanda suka kama a farfajiyar Majalisar, duk sun watsu a shafukan labarai na yanar gizo, amma kawo yanzun ba wanda suka tuhuma ballantana su gurfanar da shi a gaban kuliya.

Da yake magana da manema labarai ranar Juma’a, mataimakin shugaban kwamitin Majalisar kan harkokin yada labarai, Sanata Ben Murray-Bruce, ya yi zargin yiwuwar mutanan da ake zargin su na da daurin gindin wasu manyan Jami’an gwamnati ne.

Ya ce, “Ina tunanin dai kamar yadda aka saba, a duk lokacin da ‘yan sanda suka kama wadanda ake zargi da aikata laifi sukan gurfanar da su a gaban shari’a ne. misali, da zaran an kama masu garkuwa da mutane a kan gurfanar da su ne. Amma a ce ga wasu sun yi kumaji sun afka Majalisar kasa an kuma kama su, amma sai ba a gurfanar da su gaban shari’a ba.?

Ya wajaba ‘yan sanda su shaidawa al’ummar Nijeriya dalilin da ya sanya ba su gurfanar da su din ba, akwai mamaki da damuwa, a ce makwanni da faruwar wannan abin takaicin, amma har yanzun ba a gurfanar da kowa ba, amma da zaran an kama ‘yan kananan barayi nan da nan sai ka ji an kai su Kotu.

“Wadanda fa suka aikata wannan ta’asan a Majalisar, a wata tsaleliyar mota mai tsadan gaske kirar SUB ta kimanin Naira milyan 50 suka zo. Na bar maka sauran zancen ka yi nazari da kanka.”

Kwana guda da kawo harin, Majalisar ta zartas da cewa, za ta gayyaci Shugaban ‘yan sanda, Idris, da kuma babban daraktan hukumar DSS, Lawal Daura, su zo su yi mata bayanin yadda har hakan ta faru, a ce an afkawa Majalisa an kuma sace sandan ikon ta.

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, bayan wani dogon zaman sirri da suka yi ranar 24 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa, Majalisar Dattawan da ta Wakilai, sun zartas da cewa, za su kafa kwamitin da zai binciki dalilai da yadda aka shirya kawo farmakin.

Kwamitin kuma ana sa ran zai kwankwashi Shugaban ‘yan sanda da shugaban DSS, kan faruwar lamarin, zai kuma tattauna yadda za a samar da tsaron da ya dace a Majalisar da kewayen ta.

A ranar 26 ga watan Afrilu, da shugaban ‘yan sanda ya kasa bayyana gaban Majalisar kan dalilan kamu da tsarewar da suka yi wa Sanata Dino Melaye, da kuma yawaitan kashe-kashe a sassan kasarnan, Shugaban Majalisar Dattawan, Bukola Saraki, ya yi zargin cewa, mutanan da Buhari ya nada suna ba shi matsala sosai.

…..Majalisar ta yi azaman zartas da kasafin kudi a wannan makon.

Majalisar Dattijai ta ce, akwai yiwuwar za ta sanya hannu kan kasafin kudin bana a wannan satin, bayan da ta gama karban rahotannin kwamitocin da ta kafa.

Mataimakin Shugaban kwamitin yada labaran Majalisar kan harkokin manema labarai, Sanata Ben Murray.Bruce, ne ya bayyana hakan cikin wata ganawa da ya yi da manema labarai ranar Juma’a.

Ya ce, nazarin rahotannin ya yi nisa tun daga lokacin da shugaban Majalisar Bukola Saraki, ya umurci ‘yan Majalisar da su yi ta aiki a kansa dare da rana.

Majalisar Dattawan a ranar Laraba, ta bayyana cewa, za a gabatar da rahoton kwamitin na ta kan kasafin kudin ne a wannan makon.

Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yada labarai, Sanata Aliyu Sabi-Abdullahi, ya ce kwamitin yana kammala aikin na shi ne kan kasafin kudin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai