Connect with us

LABARAI

Sako Ga Gidan Rediyon Arewa Dake Kano (I)

Published

on


kwai wani abu muhimmi da na lura da shi ya zamo silar ci gaban duk wasu dauloli, kasashe da nahiyoyi a tsawon tarihi. Abin da ya janyo tsohuwar daular Girka ta zama babbar kasar da ta shimfida tsarin ci gaba. Kafin ita, me ya janyo kasashen Indiya da Masar sukai fintinkau a ilimi, musamman na lissafi? Me ya janyo ci gaban daular Musulinci ta Abbasiyya kuma me ya janyo faduwarta? Wani dalili ne ya janyo kasashen turawa a yanzu suka fi ko’ina ci gaba? Me ya janyo faduwar taraiyar Sobiyet (tsohuwar Russia)? Akan me ci gaba zai doru a kasashen da suke tasowa? Amsar guda daya ce kuma mai sauki, wacce kowa yana fadinta amma mai wuyar aiwatarwa. Amsar kuwa ita ce a bawa kowa ‘yancin fadar albarkacin baki, ‘yancin bayyana ra’ayi da kuma ‘yancin canja ra’ayi. Kai har ma da ‘yancin kushe wani ra’ayi ba tare da cin mutunci ko zage-zage ba. Wannan shi ne babban abin da kasashen suka doru akai. Duk kuma kasar, daular ko jamhuriyyar da take burin ci gaba to sai ta dora falsafarta akan bayyana ra’ayi. Watakila wannan shi ne abin da ya sanya aka yi wa gidan rediyon Arewa dake Kano taken “fadi ra’ayinka”.

Tsohuwar kasar Girka ta doru akan wannan falsafa ta “fadi ra’ayinka” don haka mafi yawan masu ilimin da ake tutiya da su wadanda suka assasa ci gaban ilimi daga nan suka fito. Democritus da Archimedes a Kimiyya, Plato da Epicurus a Falsafa, Aristotle a Mandiki, Socrates a iya magana, Pythagoras a ilimin “geometry” (lissafin layuka da zane-zane), Galen (Jalinus inji larabawa) a Magani (medicine) da sauransu dayawa da ba za su lissafu ba. Abin da ake da bukata shi ne mutum ya bayyana ra’ayinsa don ya isa ga masu saurare su kuma su yi amfani da hankalinsu wajen banbance aya da tsakuwa. Ta haka ne za’a samu ci gaba ta irin hanyar da Karl Mard ya gano a “Historical Determinism” kuma ya kira da “Dialectical materialism” ko kuma abin da Hegel (wanda shi Mard din ya fara samo fahimtar daga gunsa)  ya kira da “Dialectical Idealism”. A bar gaskiya tayi halinta domin a samu ci gaba, ko kuma a daurewa karya gindi don a koma baya ta hanyar abin da masu falsafar “idealism” suke kira da “Synthetics” (sakamakon da zai bayu) bayan haduwar “thesis” da kuma “antithesis”, abin da zamu iya kira a wannan siyaki kenan da gaurayewar ra’ayi don fitar da mafi karfinsu da zai bayu wajen tsara ci gabanmu. Ko kuma idan aka dauki mafi rauninsa to ga za’a koma baya.

Hatta tsarin addinin Musulinci bai haramta wani ya bayyana ra’ayi ba. Tare da cewa Allah ya san kiristoci suna cewa Annabi Isa (as) dan Allah ne, kuma ya gayamana cewa yahudawa suna kiran Annabi Uzairu (as) dan Allah, amma bai ce a hanasu su fadi ra’ayinsu ba. Hasalima, duk da yace sama sai ta yi kamar za ta kekkece don an ce Allah ya haifi da, amma haka yace a kirawo ma’abota littafi (yahudawa da kiristoci) don a tattauna da su ta nutsuwa da kyakkyawar aniya. Allah bai ce a hanasu magana ba, bai ce a hana su bude tasoshi ko shiga gidan rediyo ba kuma bai ce a kashesu ba. Ubangiji ya san cewa kisan mai wata fahimta ko hanashi magana ba ya fa’idantar da komai. Misalin yin hakan kamar misalin likitan da aka ce ya yi maganin cuta ne amma sai ya kashe mai cutar! Kuna ganin za ku dauki wannan likita a mai hankali? Tursasa biyayya ba ya kirkirar mutane masu falala sai dai ya kirkiri mutane munafukai. Don haka Allah yace babu dole a addini kuma har ya yi gaba yace duk wanda ya ga dama to ya yi imani wani kuma ya kafirce. Imani acikin zuciya yake. Hukunci yana lahira ranar da wuta za ta balbala ta kone mai kafircewa. Allah bai sanyamu mu zamo masu kareshi ba, Shi Allahn ne yake karemu tamkar yadda yake kare addininsa. Duk wata fahimta da take bukatar sai an samu masu sanya karfin jiki ko na iko wajen kareta to ba gaskiya bace. Shin gaskiya tana bukatar tsaron makaryata?

Don kada na yi nisa a shimfida, yana da kyau na fara bayyana abinda yasa na yi wannan rubutu. Wani zai tambayi me ya kawo Arewa Radio cikin bayani na kuma? Har ya iya zukalawa gaba yace ya gidan da aka kafa don bayyana ra’ayi kake wa wannan shimfida da dama sun riga sun sani? Amsar mai sauki ce. Ina tunanin wadanda suka kafa gidan rediyon sun san duk abin da nake bayani akai. Sun dora gidan rediyonsu akan falsafar ci gaba ta hanyar bayyana ra’ayi. Kuma bisa godiyar Ubangiji an samu ci gaba tun bayan kafa rediyon, ta yadda mutane kala-kala ke shiga don bayyana ra’ayinsu idan ba wasu ma’aikatan sun hana su ba. Babbar matsalar ita ce, ina kyautata zaton ba sa yi wa ma’aikatansu bita ta musamman don sanin ma’anar falsafar da suka dora gidan rediyon akai. Don kada na yi jama’u, bai kamata nace ma’aikatansu duka ba tun da yin hakan kuskure ne, ina zaton ko da ana yin bitar to akwai wani ma’aikacinsu mai suna Shehu Bala Muhammad Kabara da yake bukatar sai sun yi masa bitar musamman, daya-bayan-daya, don ya fahimci me ake nufi da yancin bayyana ra’ayi ko fadin albarkacin baki. Abin da kuma zai baka mamaki shi ne, shi fa Shehu Bala Kabara shi ne akan shugabancin kula da shige da ficen bakin da gidan rediyon suke gayyata! To idan bai fahimci wace falsafa gidan rediyon ta doru akai ba ko kuma yana amfani da damarsa wajen hana ra’ayin da ya saba da nasa fitowa a gidan rediyon, ka gayamin saboda Allah yaushe za’a samu ci gaba a rediyon?

A watan Afrilun da ya gabata, kungiyar EiE (Enough is Enough) da hadin guiwar Cibiyar Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma (Centre for Information Technology and Debelopment) suka gayyaceni don gabatar da wani shiri mai taken Zauren Dan Kasa (Office of the Citizens) da zai tattaunawa akan hanyoyin dakile tsattsauran ra’ayi acikin matasa (Countering Biolent Edtremism). Sun zabo ni saboda kasancewata mai bincike akan al’amuran da suka shafi tsattsauran ra’ayi ta fuskar addini da siyasa. Na je gidan rediyon kuma bisa godiyar Allah na gabatar da shirin tare da wata ma’aikaciyar gidan rediyon mai kirki da ake kira Binta Fulani. Na yi bayani akan illolin tsattsauran ra’ayi na siyasa da na addini kuma na bayyana banbancin da ke tsakanin “kishin addini” da kuma “tsattsauran ra’ayin addini” don kada a cakuda manufofin guda biyu. Masu bugo waya duka sun bugo kuma babu wanda yace na fadi wata magana da za ta hargitsa al’umma ko kuma ta nemi tashin hankali. A duk wadanda suka bugo wayar babu wanda ya yi tur da shirin, sai dai godiya da sa albarka. Kai ma, mai karatu, zaka iya sauraren shirin ta likau din nan don ka yanke hukunci da kanka https://kiwi6.com/file/obb1tkfzc5 .


Advertisement
Click to comment

labarai