Connect with us

LABARAI

Rashin Tsoron Allah Ya Dabaibaye Zukatan Shugabannin Yanzu -Sarkin Mota

Published

on


An nemi ‘yan Najeriya da su dawo da kishin kasa da al’umma dan samar da ingantacciyar Najeriya kamar magabata suka assasata wanda wannan hanyar kadai za ta iya ceto kasar a halin da ta ke ciki, direban Ahmad Bello, sardaunan sokoto, Alhaji Ali Sarkin mota ne yayi kiran Jim kadan bayan karban lambar yabo daga Gidauniyar Garkuwan Talban Minna Foundation da ya gudana a babban dakin taro na tunawa da tsohon mai shari’a Idris Legbo Kutigi da aka yi asabar din makon da ya gabata.

Sarkin mota yace rashin adalci da zaluncin da su ke yiwa kasa yasa a yau ba wani abu da ke da muhimmanci gare su da ya wuce bin bokaye da likitoci ba tare da sun san matsalar da ke damunsu.

‘Yan siyasa sun manta da cewar karfin kuri’a ce ta kawo su, maimakon su mayar da hankali wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da samar da ayyuka ga jama’a sun mayar da hankali wajen karkatar da dukiyar gwamnati zuwa aljihunsa. Najeriya tayi rashin shugabanci wanda dole sai an samu masu kishin kasa da al’umma, wanda ya zama dole a cire bambancin addini da kabilanci sannan za a dawo akan turba.

Zama na da marigayi sardauna na ga irin kwazo da himmar da sanya wajen gina kasar nan. Idan ka kwatanta irin salon mulkin da ake tafiyarwa yanzu tuni an raba hannu riga wajen shugabanci na gari, ban cin gaggawar bada kwangiloli da ‘yan siyasar da masu mulkin ke gaggawar baiwa kawunansu ba wani abinda ya rage a tafiyar.

Maganar mafita, hanya daya ce samar da shugabanci na adalci a kasa, tafiyar da mulkin siyasar yadda ya dace ba tare da son zuciya ba.


Advertisement
Click to comment

labarai