Connect with us

MANYAN LABARAI

Melaye: Saraki Da Dogara Sun Kai Wa Buhari Karar ‘Yan Sanda

Published

on


A jiya ne Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da takwaransa na Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, sun kai karar Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris ga Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.

Karar ta wadannan shugabannin majalisa dai ta biyo bayan tirka-tirka da ke ci gaba da wakana tsakanin rundunar ‘yan sandan Nijeriya da Sanata Dino Melaye ne.

Saraki da Dogara sun bayyana batun kai karar ‘yan sandan ga Shugaba Buhari ne jim kadan bayan kammala wata ganawar sirri da suka yi da Shugaban Kasar. Inda suka ce, sun sanar da Shugaba Buhari batun kin bayyana gaban majalisar da Babban Sufeton yayi har sau biyu.

Sun ce; “Mun tattauna ne dangane da batun ‘yan sanda. Sannan kuma mun yi magana dangane da kunnen uwar shegun da Babban Sufeton ‘Yan sanda yayi na kin bayyana a gaban majalisa.

“Wannan babban abin damuwa ne, kuma dole ne a dakile batun. Yana da kyau rundunar ‘yan sanda ta fahimci cewa ita ma fa karkashin dokokin Nijeriya take.” inji su.

Shugaban Majalisar Dattawa ya ce, sun kai wannan ziyarar ne bisa gayyatarsu da Shugaban Kasa yayi. Ya kuma bayar da tabbacin cewa za su zartas da kasafin kudin bana a makon da za a shiga.

 


Advertisement
Click to comment

labarai