Connect with us

LABARAI

‘Mahaifiyar Sakataren Yan Jarida Ta Kasa Ya Yi Jajen Rasuwar Shugaban NUJ

Published

on


Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa Mr. Waheed Odusele ya jagoranci tawagar mambobin ‘yan jarida a daga sassan daban-daban na kasar nan zuwa ga kai gaisuwar jajantawa wa iyalan mahaifiyar  mahaifiyar Sakataren Janaral na kungiyar ‘yan jarida ta kasa Shui’abu Usman Leman a Bauchi, a bisa mutuwar da ta yi kwanakin baya.

Mahaifiyar sakataren dai ta mutu ne a kwanakin baya, inda aka yi mata gagarumin bikin bisa da kaita makabarta a ranar Asabar din nan da ta gabata, inda ‘yan jarida da daman gaske daga jahohi da daman gaske a karar nan suka shaidi bikin bison.

Tawagar shugaban ‘yan jaridan wadanda suka kuma yi tattaki har zuwa gidan marigayiyar inda suka gaida makusantanta da kuma nuna alhenin rashinta.

Da yake mika ta’aziyyar a madadin dukkanin ‘yan jaridan da suke Nijeriya, shugaban Waheed Odusele ya nuna alheninsa na rashin Mama, yana mai addu’ar Allah ya baiwa makusanta da ‘yan uwanta hakurin jure rashin mahaifiya.

Sauran ‘yan jaridan da suka rufa wa shugaban baya sun hada da, mataimakinsa na matakin kasa Kwamared Muktar Gidado, shugaban kungiyar marubuta labarin wassani na jihar Bauchi, Umar Sa’idu, shugaban kungiyar ‘yan jarida na jihar Bauchi Kwamared Ibrahim Malam Goje, da sauran jagoririn ‘yan jarida a matakan jiha da kasa.


Advertisement
Click to comment

labarai