Connect with us

LABARAI

Likitocin Nijeriya Da Na Kasashen Waje Sun Fara Bada Agaji Kyauta A Kebbi

Published

on


 

 

Gwamnatin jihar kebbi tare da hadin gwiwar “Moses Lake Medical Team  sun fara bada ayyukan kiwon lafiya a kyauta a jihar ta kebbi.

Likitocin da kuma ma’aikatan jinyar sun sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa na Sir Ahmadu Bello da ke a Birnin-kebbi daga kasashen waje domin kawai su bada ayyukan kiwon lafiya a kyauta ga jama’ar jihar kebbi wanda gwamnatin jihar tayi hadin gwiwa da su kan shirin da ta fito dashi a cikin jihar domin tallafawa jama’ar ta kan harakar lafiya a jihar.

Tawagar likitocin sun samu tarbo daga kwamishinan kiwon lafiya na jihar ta kebbi Alhaji Umar Usman Kambaza, Daktocin ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar da kuma sauransu.

Da yake bayyana wa manema labaru yayi fara shirin  ayyukan kiwon lafiya a kyauta a jihar ta kebbi Dakta Aminu Haliru Bunza kuma shine daraktan kiwon lafiya na ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar kebbi yace” fiye da likitoci 90 na Najeriya da na kasashen waje da kuma ma’aikatan jinya 100 da kuma ma’aikatan gwaji kashe,  fitsari da kuma jini arba’in da kuma sauran wasu ma’aikata masu taimakawa wurin ganin shirin bada kiwon lafiya a kyauta na jihar kebbi yasamu nasara”. Dakta Bunza ya ci gaba da cewa “ ana saran isowar wasu likitoci kimanin 60 a jihar ta kebbi mako mai zuwa” . Ya kuma ce “wannan shirin bada kiwon  lafiya a kyauta da aka shiriya a jihar ta kebbi wannan shine Karo na hudu kenan gwamnatin jihar na shirya shirin ga jama’ar jihar domin tallafa musu wurin ganin cewa an inganta kiwon lifayar al’ummar jihar”.

Dakta Aminu Haliru Bunza ya bayyana hakan ne a lokacin da aka fara bada shirin kiwon lafiya a kyauta a asibitin gwamnatin jihar ta kebbi da ke garin kalgo a yayi zantawa da manema labaru a ofishinsa da ke  a Kalgo a jiya.

Ya kuma kara bayyana wa jaridar LEADERSHIP A Yau  da cewa likitoci na kan duba marasa lafiya masu ciwo iri daban daban daga kowace karamar hukumar mulki 21 da ke cikin jihar ta kebbi wanda  zasu ci gajiyar wannan shirin bada kiwon lafiya a kyauta a jihar da gwamnatin jihar ta shirya a karkashin jagorancin gwamnan jihar sanata Abubakar Atiku Bagudu.

Bagu da kari yace “ wannan shirin na kiwon lafiya a kyauta da ake gudanar wa a halin yanzu  a asibitin gwamnatin jihar ta kebbi da ke garin kalgo za’a kwashe kimanin sati biyu zuwa uku a bayar da kiwon lafiya a kyauta a jihar ta kebbi”.  Saboda haka yayi kira ga masara lafiya da kuma uwaye da su tabbatar da sun samu cin gajiyar wannan shirin kiwon lafiya a kyauta.

Daga nan ya godewa gwamnatin jihar kebbi kan irin kokarin da ta keyi wurin ganin ta bada tallafin kiwon lafiya a kyauta ga jama’ar wannan jihar


Advertisement
Click to comment

labarai