Connect with us

LABARAI

Kasa Da Kashi 40 Na Masu Juna Biyu Ke Samun Daman Haihuwa A Asibiti UNFPA, NANNM

Published

on


Gidauniyar tallafa wa al’umma na Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA), da kuma kungiyar Likitocin Anguwarzoma ta kasa da masu karban haihuwa (NANNM), sun bayyana a karshen makon nan cewa, kasa da kashi 40 ne na mata masu ciki a Nijeriya suke samun damar zuwa asibiti su haihu, domin da yawan su sun gwammace su haihu a gida, kasantuwar rashin kwararrun ma’aikatan na lafiya.

Jami’in shirya shirin, na mata masu ciki a Nijeriya na Majalisar ta, UNFPA, Dakta Rabi Sagir, da shugaban kungiyar ma’aikatan Nas-Nas masu kula da kananan yara (NAPAN), Uwargida Olubunmi Ayedun, ne suka bayyana hakan a wajen wani shirin wayar da kai da kungiyoyin na, UNFPA da NANNM, suka shirya a Abuja, domin bukin ranar Anguwarzoma na shekarar 2018.

Shirin, a cewar Dakta Sagir, an yi ne domin wayar da kan Matan da suka kai shekarun haihuwa da su rika ziyartan wuraren awon ciki da zaran sun dauki ciki. A kuma karfafa wa Mata da Maza bakidaya da su rika zuwa asibitoci domin auna matsayin lafiyar su da zaran sun ji ba daidai ba.

Dakta Sagir ta kara da cewa, “Mun taru ne domin bukin ranar Anguwarzoma ta duniya, wacce ake yi a dukkanin ranakun 5 ga watan Mayu duk shekara, domin nu na irin gudummawar da ma’aikatan Anguwarzoman ke ba da wa wajen ceto rayuwar Mata da Kananan yara.

“Ma’aikatan Nas-Nas da Anguwarzoma na Nijeriya tare da hadin gwiwar UNFPA, suna gudanar da ayyukan lafiya ga wadanda ba sa iya samun su, matalauta da kuma marasa galihu. Su na kuma bayar da agajin awon ciki, gwajin jini, su na kuma baiwa kananan yara kulawar da ta dace kan bukatun su na lafiyar su.”

Kan nu na hali marar kyau da wasu ma’aikatan na lafiya ke yi kuwa, Dakta Sagir ta ce, UNFPA, ta gano cewa halayar banza na ma’aikatan lafiyan yana iya yin illa ga marar lafiyan da ya zo neman lafiyar, zai kuma iya shafan aikin na su ma bakidaya.

Kan haka, UNFPA tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi na duniya sun kaddamar da wani shiri na nu na girmamawa ga masu ciki domin a kara kyautata halayyar ma’aikatan na kiwon lafiya. Shirin an yi shi ne domin ganin ma’aikatan na lafiya su na girmama marasa lafiya, a kuma nu na masu cewa, marasa lafiyar fa su na da hakkin samun lafiyar.”

A na ta jawabin, Uwargida Aye Fun, cewa ta yi, “Lokutan daukan ciki su na da mahimmanci sosai kuma lokuta ne da ke da bukatar kulawa sosai. Shi ya sanya a matsayin mu na ma’aikatan Anguwarzoma na Nijeriya, mu ka zo nan domin mu wayar wa da Mata kai kan yadda za su kula da kananan yaran su.

 


Advertisement
Click to comment

labarai