Connect with us

LABARAI

Gidauniyar Shaikh Dahiru Bauchi Ta Horas Da Ma Su Tafsiri 43

Published

on


 

 

A ranar Alhamis da ta gabata, gidauniyar Shekh Dahiru Usman  Bauchi (SHEKH DAHIRU BAUCHI FOUNDATION) ta jagoranci kammala koyon tafsirin Alkur’ani mai girma ga wasu daliban ilimi, inda suka sami ilimim yadda ake tafsirin Alkur’ani mai girma a wannan cibiya.

A sakonsa wajen taron, Shekh Dahiru Usman Bauchi, ya nuna matukar jin dadinsa na yadda wannan gidauniya ta tashi tsaye na ganin ta samar da malamai da za su rika tafsirin Alkur’ani mai girma a lokutan watan Azumi.

Shekh Dahiru Bauchi wanda ya sami wakilcin daya daga cikin ‘ya’yansa, Malam Bashir Dahiru Usman Bauchi, ya  bukaci wadanda suka kamala karatun da su kara tashi tsaye wajen neman ilimin addinin musulunci da za su sami damar yin fassarar kamar yadda addinin musulunci ya tsara.

Ya kuma tunatar da su cewar, yanzu za su fara samun tambayoyi daga al’umma r musulmi kan al’ummurran da suka shafi addinin musulunci, karatun da suke, a cewar malam, shi ne zai sa su sami damar sauke nauyin da aka dora ma su a cikin sauki.

Shi ko Malam Sunusi Kutama, cewa ya yi, an fara koyar da tafsirin ne a wannan cibiya a shekara ta 2015, wanda aka fara yaye dalibai 36, zuwa yanzu, kamar yadda ya ce, a wannan yayen malaman an tabbatar da malamai bakwai da suka sami sami ilimin fassarar Alkur’ani mai girma a wannan cibiya ta Shekh Dahiru Usman Bauchi da ke garin Kaduna.

Wadanda aka kammala koya ma su yadda za su yi tafsirin Alkur’ani mai girma, sun fito ne daga jihohin Kaduna da Katsina da Neja Da Nasarawa da Abuja da sauran jihohin da suke sassan Nijeriya ba arewacin Nijeriya kawai ba.

Zuwa yanzu wannan cibiya ta koyar da yadda ake yin tafsirin Alkur’ani mai girma, a cewar Malam Sunusi Kutama, sun bude makarantu uku a kasar gana, ya ce za a ci gaba da budewa a sauran kasashen Afirika baki daya.

A karshe, Malam Sunusi Kutama ya ce, wannan cibiya na shirye ta amsa bukatar duk jihar da ke Nijeriya, da suke son a bude ma su wannan gidauniya ta koyar da Tafsirin Alkur’ani mai girma.


Advertisement
Click to comment

labarai