Connect with us

LABARAI

APC Ta Ce Zaben Mazabunta Ya Gudana Cikin Nasara

Published

on


Duk rahotannin samun tashin hankula da zargin tafka magudi a Jihohi da yawa, inda Jam’iyyar APC,  ta gudanar da zabukan mazabun ta, Jam’iyyar ta bayyana cewa, zabukan sun gudana “lami lafiya.”

An samu rahotannin tashe-tashen hankula da aikata magudi a Jihohi da yawa da suka hada da Bauci, Delta, Ebonyi, Enugu, Oyo, Abiya, Imo da Jihar Ribas.

An sami rahotannin kashe akalla mutane daidaya a Jihohin Ribas da Delta, inda kuma aka kona Sakatariyar wata Karamar Hukuma a Jihar Bauci, lokacin gudanar da zaben.

A wasu Jihohin kuma, kamar Enugu, Oyo da Ebonyi, an zargi Jami’an Jam’iyyar da yin magudi a wajen zaben.

“Sam yanda aka gudanar da zaben bai yi ba,” in ji Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin a Jihar Enugu.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun Sakataren ta na yada labarai na kasa, Bolaji Abdullahi, Jam’iyyar ta APC, cewa ta yi zabukan sun gudana ‘sumul kalau.’

Ya kuma yaba wa wakilan kwamitin shirya tarukan kan gaskiyan su da kuma mayar da hankalin su kan shirya zabukan.

Amma ya yarda da cewa an sami matsaloli a wasu Jihohin, sai ya yi kira ga ‘ya’yan Jam’iyyar da su kasance ma su bin doka, su kuma nufi kwamitocin sauraran koken Jam’iyyar na Jihohi ne kan duk abin da wani ke jin ba a yi ma shi daidai ba.

“Mun san an sami wasu matsaloli a wasu Jihohin wajen gudanar da zabukan. Kan haka ne muka kafa kwamitocin da za su fara zama ranar Litinin 7 ga watan Mayu 2018, domin sauraron koken dukkanin wadanda suke jin ba a yi ma su daidai ba.

“Kan haka muna kira ga dukkanin ‘ya’yan Jam’iyyar mu da su kasance masu bin doka a duk inda su ke jin ba a yi masu daidai ba, ta hanyar kai koken su ga wadannan kwamitocin na Jihohin su.”

 


Advertisement
Click to comment

labarai