Connect with us

LABARAI

Ana Nada Sarkin Fawan Kasuwar Sabon Garin Zariya

Published

on


Mai girma Iyan Zazzau, Alhaji Muhammad Bashar Aminu ya nada Alhaji Adamu Dan-Daurawa a matsayin Sarkin Fawn Kasuwar Sabon garin Zariya a jihar Kaduna.

A jawabinsa bayan kammala nadin sabon sarkin fawan Sabon garin Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu ya bukaci sabon sarkin fawan day a nada da ya yi duk abin da ya dace domin ciyar da wannan sana’a ta fawa gaba, tare da tattalin zaman lafiya ga duk mutanen da za su kasance a

karkashinsa, a matsayinsa na sarkin fawa.

Iyan zazzau ya kuma yi kira ga duk ma su sana’ar fawa da suke kasuwar Sabon gari, da su hada kai da sabon sarkin fawan domin ci gaban wannan sana’a da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a cikin wannan sana’a ta fawa a kasuwar sabon gari.

A zantawar da wakilinmu ya yi da sabon sarkin fawan sabon garin Zariya, Alhaji Adamu Dan-Daurawa, ya nuna matukar jin dadinsa ga mai girma Iyan Zazzau, day a tabbatar da shi a matsayin Sabon sarkin fawan kasuwar Sabon garin Zariya.

Kamar yadda ya ce, zai dauki wannan dama da Iyan Zazzau ya ba shi, na ganin ya yi duk mai yiwuwa, wajen ci gaban wannan sana’a ta fawa da kuma hada kan mahauta da suke gudanar da sana’ar fawa a wannan kasuwa.

Sabon sarkin fawan kasuwar sabon gari, Alhaji Adamu, ya yi amfani da damar day a samu, inda ya yi kira ga daukacin ma su sana’ar fawa a wannan kasuwa, da su ba shi dukduk goyon bayan da suka dace, domin ya sami saukin sauke nauyin da aka dora ma sa, na Sabon sarkin fawan kasuwar Sabon garin Zariya.

Ya kammala da cewar, zai yi duk abin day a kamata, na ganin ya ciyar da ma su sana’ar fawa gaba, tare kuma da kafa wasu kwamitoci da za su zama silar bunkasar wannan sana’ar da kuma wadanda ke yin sana’ar a wannan kasuwa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai