Connect with us

LABARAI

An Bude Masallacin Juma’a A Unguwar Malam Atiku-Tankarau

Published

on


A ranar Juma’a da ta gabata, mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya jagoranci bude masallacin juma’a a garin Unguwar Atiku-Tankarau ta gundumar Dutsen-Abba a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.

Alhaji Shehu Idris ya yaba wanda ya gina masallacin , na yadda ya yi amfani da dukiyarsa wajen ciyar da addinin musulunci gaba.

Mai martaba sarki wanda Mukaddas na Zazzau, Malam Balarabe Yahaya ya wakilta a lokacin bude masallacin, ya yi kira ga al’ummar musulmi , masu dukiya nah alas, das u yi koyi da wanda ya gina masallacin, wajen amfani da dukiyarsu wajen ciyar  da addinin musulunci gaba ta ko wane fanni.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Unguwar Malam Atiku da sauran garuruwa da suke makotaka da wannan gari, da su raya wannan masallaci da yin ibada da kuma yin karatun addinin musulunci.

Shi ma a jawabinsa a wajen taron bude masallacin Hakimin Dutsen Abba Maharin Zazzau, Alhaji Falalu Umar, ya nuna matukar jin dadinsa da yadda wannan bawan Allah ya gina wannan masallaci a wannan gari na Unguwar Malam Atiku.

A da jawabinsas, Maharin Zazzau, ya ya jinjina wa mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, na yadda ya ke bayar da gagarumar gudunmuwa, , na ciyar da addinin musulunci gaba, da kuma tabbatar da zaman lafiya a masarautar Zazzau da jihar Kaduna da kuma Nijeriya baki daya.

Sarkin filanin Zazzau, Abdulkadir Tankarau, wanda ya jagoranci ginin masallacin, ya ce, tun da aka fara ginin masallacin bai taba yin tozali da wanda ke ginin masallacin ba har zuwa wannan rana rana da aka kaddamar da ginin masallacin.

Sai dai kuma ya yaba wa wanda ya gina masallacin tare da yin alkawarin ci gaba da amfani da masallacin kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen kaddamar da masallacin sun hada da Malam Shu’aibu Hayin Tsauni [ Alhajin Badi] da Malam Hadir da kuma Sarkin Samarin Dutsen-Abba, Alhaji Haliru Jibrin, wanda duk sun yaba wanda ya gina masallacin a wannan gari na Unguwar Malam Atiku .

Wannan taro ya sami halartar sarakunan Tankarau da Unguwar Ale da Unguwar Wakilin Hatsi da Majeru da Dallatu da fam-madina da dai sarakuna da suke wannan Gunduma ta Dutsen-Abba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai