Connect with us

LABARAI

Abin Da Buhari Ya Fadi Min Dangane Da Zabukan APC Da Suka Gudana –Okorocha

Published

on


 

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri a garin Daira tare da gwamnonin jihar Imo dana Zamfara, Rochas Okorochas da Abdulaziz Yari.

Jami’in watsa labaran shugaban kasar ne Bashir Ahmad, ya tabbatar da ganawar da suka yi a shafisa na Twitter ranar Lahadi.

Ya ce, “A yammacin yau ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo.’’

Mista Okorocha, ya yi bayani ga maneman labarai bayan tataunawar da suka yi da shugaban kasa, inda ya ce, ya yi wa shugaban kasar bayani ne na sakamakon zaben mazabu da aka gudanar na jam’iyyar APC a fadin tarayyar kasar nan.

Ya nuna takaicinsa a kan yadda ‘yan jam’iyyar suka suka gudanar da zaben a wasu jihohin kasar nan, ya kara da cewa, jam’iyyar zata yi maganin irin wadanna halin a nan gaba.

Mista Okorocha ya kara da cewar, “Muna bukatar dimokradiyyar cikin gida da cikin ja’iyyarmu, hakan ne kuma hanyar daya fi dace wa, irin wanna halin beran ba zai kaimu ko ina ba, halin sace akwatunan zabe da sace sakamakon zabe a wasu wurare, dole a dakatar da ire iren wadannan halayen”

“Na yi wa shugaban kasa bayani, mun kuma yi itifakin cewar, dole a dakatar da irin wadanan halayen”

A kan bayanin da shugaban kasan ya yi masa, gwamnan ya ce, “Ya bayana cewar lallai zai yi kokarin ganin an dakatar da irin wanna halayen a jam’iyyar, ba wai magana jihar Imo kadai bane, kasar ne gaba daya, muna bukatar dimokradiyyar a cikin gida, ta haka ne za a samar da mutunta juna a cikin jam’iyya”

A nasa tsokacin gwamnan jihar Zamfara MistaYari, ya bayyana cewar, zaben da aka gudanar a yankin Arewa maso yammacin kasar na ya tafi a bisa tsari da kwanciyar hankali.

Ya ce,“Ya kamata a sani cewa, a harka dimokraddiya, ba zai yiwu komai ya tafi dari bisa dari ba amma a bisa bayanan dake isowa garemu komai ya tafi lafiya kalau a jihohin Katsina da Kebbi da Sokoto da Zamfara da kuma jihar Kano, wuraren da mutane ke tunanin za a samu matsala nan ma an yi lafiya kalau.

“Amma duk wani dake wani korafi, to a kwai kwamitin da uwar jam’iyyarmu ta kasa ta kafa, mutun na iya kai kokensa domin a bi masa kadin kukan nasa.”

Kanfanin dillancin labarai na NAN ta lura da cewar, a kwai rudani dabam dabam a kan yadda aka gudanar da zaben unguwanni na jam’iyyar APC a fadin tarayyar kasar nan.

An samu mummunan arbatu a jihar Delta, inda hukumar yan sanda ta tabbatar da mutuwar wani dan takarar shgabancin jam’iyyar a karamar hukumar Ughelli South ta jihar.

Jami’in watsa labaran rundunar yansanda, Andrew Aniamaka, ya ce, an dabawa Jeremiah Oghobeta, har ya mutu a mazabar Jeremi Ward 3, Okwagbe.

Zaben unguwannin ya gudana ne a ranar 6 ga watan Mayu maimakon ranar 5 ga watan Mayu a jihohin Adamawa da Oyo saboda rikice rikicen siyasa a stakanin masu ruwa da tsaki a jihohin.

A samu rudani a yanayin da aka gudanar da zabe ranar Lahadi, saboda yayin da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustafa, ke bayanin cewa, zabukkan sun gudana lami lafiya, shi ko Nuhu Ribadu cewa ya yi zaben bai gudana a unguwarsa na Bako a Yola ba. Mista Mustafa ya yi nasa zaben ne a unguwan Gwadabawa dake Jimeta Yola.

Bayani ya kuma nuna cewa, wani bangaren jam’iyyar APC a jihar Kebbi sun gudanar da zangazangan lumana a babban ofoshin jam’iyyar dake Birnin Kebbi suna nuna rashin amincewarsu a kan shirin da aka yin a amincewa da wadanda aka zaba kai tsaye ba tare da anyi zabe a mazabu 225 dake fadin jihar.

Masu zangazangan suna dauke ne da kwalayen da aka yi rubutu daban daban kamar “Bamu yarda da rashin yin zabe ba a jihar Kebbi’; `Muna bukatar Adalci a cikin jam’iyya’ da sauransu.

Shugaban masu zangazangar Adamu Gulma, ya bayana wa maneman labarai a ofishin jam’iyyar cewa, “Abin daya farua jihar Kebbi ba zabe bane,taro ne da gwamnati da wasu masru da tsaki suka yi domin biyan bukatunsu”

Amma kuma a reshen jam’iyyar ta APC ta jihar Ondo an yaba wa yadda aka gudanar da zaben unguwannin ne a fadin mazaba 203 dake fadin jihar ranar Asabar.

Yake fitowa daga sassan jihar sun nuna lallai an gudanar da zabubbukan cikin nasara a Jami’in watsa labaran jam’iyyar, Abayomi Adesanya, ya bayyana wa maneman labarai cewa, bayanan da yake fitowa daga fadin ya nuna an yi zaben cikin nasara.

Kanfanin watsa labarai na NAN ta lura cewar, an gudanar da zaben unguwannin lami lafiya a jihohi da dama a fadin tarayyar kasar nan, kamar jihohin Lagos da Kaduna da Gombe da Ogun da Nasarawa da Plateau da Taraba da Borno da kuma jihar Yobe.

A ranar Lahadi jam’iyyar ta kirayi ‘yan jam’iyyar da aka cutar ko kuma suke da wani kotafi dangane da zabubbukan da aka gudanar ranar Asabar dasu mika koken nasu ta hannun kwamitin da aka kafa don jin koken daya danganci zaben a fadin tarayyar kasar nan.

Jami’in watsa labaran jam’iyyar, Bolaji Abudulahi, ya bayar da sanarwa haka a garinAbuja, ya kuma taya wadanda aka zaba murna nasarar da suka samu, yana mai cewar, lallai gaba daya an gabatar da zaben cikin nasara a mafi yawan jihohin tarayyar kasar nan.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai