Connect with us

LABARAI

Zagi Ko Cin Zarafin Shugabannin Ba Alheri Ba Ne –Fatahu

Published

on


An kira ga matasa da ke shiga da su kare kuri’unsu ta hanyar zaben shugabannin na gari, domin sai ka zabi shugaba na gari mai amana sannan zai yi tunanin dora ka akan turba. Alhaji Fatahu Ahmed Kontagora ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a minna.

Domin ita siyasa abu ne ra’ayi kuma ba wanda zai shiga siyasar ba dan ya karu ba, idan mutum yace ba haka ba ne to ya boye gaskiya don duk mutumin da ya bi jama’a kuma ya nemi goyon baya a wajen su ya kamata ya cika alkawurran da ya dauka idan yaci zabe in kuma ya yana tunanin hakan da ya yi kamar wata hikima ce ta yaudara to ya yi kuskure babba, domin bayan tiyar akwai wata cacar, lokaci zai yi da in har da rai da lafiya sai ya sa ke dawo wa neman alfarma, ba na jin a lokacin zai sake dawowa dan wata yaudarar kuma, don haka ina jawo hankalin matasa ‘yan uwana da mu rika kai zuciya nesa, mu zama masu hakuri da juriya kar mu yarda mu sake bacin rai na jefa mu a turbar da ba ta dace ba.

Yanzu lokacin zabuka na karatowa mu zauna mu wayar da kan junan mu, mu dubi inda aka samu kurakurai dan gyarawa kar mu yarda ‘yan siyasa na amfani da mu wajen bata rayuwar mu, duk wanda yake ganin ya yaudare mu, to lallai mu dauka kan shi ne ya yaudara ba mu ba.

Ni fa banga alfanun bangar siyasa ko zagin shugabanni ba, ban ga kuma alfanun shaye-shaye a tsakanin mu ba, domin bangar siyasa ko shaye-shaye ba za ta tsinanawa rayuwar ka da komai ba, wasu ‘yan siyasa na tunanin yaudara da zalunci kamar shi zai kai su ga tudun natsira wanda wannan kuskure ne babba, hakan kuma kar ya tunzura mu ya kai mu ga fadawa mummunar yanayin da zai sa mu fita hayacin mu.

Mu tabbatar in zabuka sun zo mun kwantar da hankalin mu wajen zaben mutum in kirki da taimaki rayuwar mu, wanda zai bada lokaci wajen sauraren korafe-korafen mu, wanda kasar ce da cigabanta a zuciyar shi amma idan mun yarda da banga, fadanci to mu tabbatar inda muka fito can zamu koma. Yau a kasar nan ba wanda aka fi amfana da shi irin matashi amma kuma kullun mu ne a baya, lokaci yayi da zamu yi kaimu kiyamul-laili mu nemarwa kan mu mafita, mafitan nan ba sai mun rika makami ba, makamin mu shi ne kuri’armu.

Don haka kar mu yarda bacin rai ya samu aikata abinda zai kai ga jefa mu a danasani domin bai dace ba matashin da ake tsammanin zai zama haske a gaba ya bata rayuwarsa tunda kurciyarsa, ina kira ga ‘yan uwana matasa in har da gaske muke yi to mu tabbatar mun inganta rayuwar mu tunda kurciyarmu, siyasa ba hauka ba ce duk yadda ka ke ganin an cuceka dan an yi amfani da kai bayan nasara an watsar da kai, to ka rike kimarka kul ba jima sai an dawo gare ka.

 


Advertisement
Click to comment

labarai