Connect with us

LABARAI

Stars Foundation Ta Bada Kyautar Irin Masara Ga Manoma A Chimbi

Published

on


Gidauniyar Stars Foundation ta sha alwashin baiwa kananan manoma ilimin nema da tallafi irin masara ta hanyar zamani kyauta. Shugabar gidauniyar Hajiya Zarah I. Abdullahi ta bayyana hakan a lokacin da take bayani ga kananan manoma sama da mutum dari da doriya da suka halarci taron da ta shirya a makaranta faramare na garin Chimbi da ke karamar hukumar Paiko da ke jihar Neja.

Taron wanda aka yiwa taken ‘ Karin haske ga noma mafi tsafta da zata iya samar da sanadarin abinci mai anfani’. Shugabar ta cigaba da cewar ganin yadda gwamnati ta jawo hankalin jama’a kan dawo da martabar noma, bai kamata a bar jama’a kare zube ba hakan yasa Stars Foundation zakulo masana dan bada lokacin su wajen wayar da manoma ta yadda zasu iya cin moriyar anfanin nomansu.

Da yake karin haske, wani jigo a harkar noma kuma mataimakin shugaban kungiyar manoma shinkafa (RIFAN) ta jiha, Malam Isyaku Bn Yusuf Kontagora, ya tabo batutuwa da suka shafi yadda ake huda da gyaran gona da kuma yadda ake shukin masara, wanda yace idan dai za a bi wannan tsarin a hekta daya kwatankwacin filin kwallo za a iya samun buhu tamanin da takwas na masara. Yace a wannan tsarin da ake akai idan manomi zai iya bin wannan tsarin ba zai kashe sama da dubu dari a aikin hekta daya ba,  koda akan dubu bakwai aka sayar da buhun masarar da noma a irin wannan tsarin manomi zai iya samun anfanin gona na a kallan dubu dari shida da goma sha shida koda za a sayar da buhun masara akan dubu bakwai ne.

Malam Isyaku ya bayyana illar da takin zamani yake yi ga lafiyar dan Adam, amma tsarin sanadarin noma na zamani abu ne mai anfani, abubuwan da aka samar a wannan sanadari ba abu ne mai cutarwa ba maso ma yana dauke da sanadarin bitamin ‘A’ da zai taimakawa jikin dan Adam.

Da yake bayani ga wadanda suka halarci taron, mataimakin darakta a ma’aikatar gona ta jihar Neja, Malam Adamu Maikasuwa ya bayyana cewar gwamnatin jiha ta samar da shirin noma wanda hadin guiwa ne tsakaninta da gwamnatin tarayya ga ‘yan shekaru sha takwas zuwa talatin da haihuwa. Shirin wanda gwamnatin jiha ta samar filayen noma da za a baiwa kowani matashi hekta daya tare da tallafi wanda bayan an kai ga kakar girbe abincin gwamnati ne za ta samar da ‘yan kasuwan da za su saye anfanin gonar.

Maikasuwa yace yanzu haka gwamnatin jiha ta samar da motocin noma wanda za a rika bada shi haya ga duk manomin da ke bukata.

Gidauniyar dai ta rabar da irin masara kyauta mai dauke da sanadarin bitamin ‘A’ kyauta ga mahalarta taron su a kallan dari da bakwai. Da take karin haske, Shugabar gidauniyar, Hajiya Zarah I. Abdullahi tace masana kuma manazarta harkar noma su din ne suka samar da wannan sabon irin duba da yanayin jikin dan Adam, wanda idan manoma suka rungumi wannan sabon tsarin noman masarar zai anfanar da su kuma za su samu alheri mai dinbin yawa.

Da daman mahalarta taron bitar sun yaba kuma sun nuna gamsuwarsu da wannan sabon sanadarin da shan alwashin rungumar wannan tsarin.

Taron dai ya samu wakilcin ma’aikatar gona ta jiha, da manyan masana harkar noma, sai Daga cin Chimbi, Alhaji Abdulkarin Danladi.


Advertisement
Click to comment

labarai