Connect with us

LABARAI

Shugaban Kwalejin Kimiyya Ta Tarayya Dake Bauchi Ya Gargadi Dalibai Kan Shigar Banza

Published

on


Shugaban kwalejin kimiyya da fasaha hade da kere-kere na gwamnatin tarayya da ke Bauchi, Arch Sunusi Gumau ya gargadi dukkanin daliban kwalejin da su ke kaurace wa sanya tufafin da basu dace ba, hade da kaurace wa munanan dabi’u da shiga wasu bangaren da ka iya kawo wa kwalejin tashin-tashina.

Ya bayar da gargadin tasa ne a lokacin da ke jawabi a karshen mako a wajen wani taro wayar da kai kan dokoki da ka’idojin shigar (tufafin sanyawa) da kwalejin ta aminta da shi wanda daliban koyon aikin jarida masu karanta babban diploma wato HND na kwalejin suka shirya domin yin tilawa kan shigar da ta dace da kwalejin bisa dokokin kwalejin.

Gumau ya jinjina wa kyakkyawar tunanin daliban na shirya irin wannan taron da zai fadakar, yana mai kira a garesu da su ci gaba da bin dokokin daukan darasi daga wajen malaman kwajein domin samun sakamako mai kyau da kuma nuna dabi’u mai kyau a lokacin da suke daukan darasi domin fahimtar ababen da ake son su koya.

Ya kuma shawarci bangarorin biyu, da cewar su ci gaba da kulla kyakkyawar alaka a tsakanin malamai da dalibai kamar ta ‘da da ubansa’ domin kyautata koyo da kowarwa a cikin kwalejin kimiyyar.

Sanusi Gumau ya ce, “Babu wani dalibi da zai bayar da cin hanci ko kuma bayar da kai wajen yin zina da daliba don neman sakamako mai kyau a wajen wani malamai. Dukkanin wani dalibi ko dalibar da hakan ta faru da su su kawo mana rahoto cikin gaggawa domin daukar mataki daidai da dokar kwalejin. Dukkanin batun amsar cin hanci ko kuma keta haddi na neman yin zina da daliba a kai wa hukumar gudanarwa rahoton aukuwar hakan cikin gaggawa,” Ya sake nanatawa.

Don haka ya bayyana cewar za su ci gaba da yin duk mai iyuwa wajen daukaka darajar ilimi da kuma ci gaba da kokarinsu wajen kenkeshe hazikan dalibai a kowani lokaci.

Tun da fari, jagoran tawagar masu shirya taron bita kan dokokin sanya tufafin kwalejin, Abubakar Umar ya bayyana cewar sun yi wannan gagarumar aikin ne domin fadakar da daliban da suke rayuwa a cikin makarantar domin kada suke kauce wa dokokin kwalejin walau da saninsu ko kuma a bisa akasinsa domin kada su fuskacin fushin masu lura da hakan.

“Daliban koyon ilimin aiki jarida, a kowani lokaci fatansu kasancewa ‘yan jarida ne, aikin dan jarida kuma akwai fadakarwa, ilmantar da jama’a domin a dacewa da ababen da suke da kyau. Wannan dalilin ne sanya mu muka yanke shawarar taimaka wa hukumar gudanarwa na kwalejin wajen ci gaba da fadakar da daliban ababen da za su taimaki kowa da kowa wajen daukan darasi da kuma bayar da shi ba tare da ana samun kai ruwa rana a tsakanin daliban da kuma malamansu ba,” In ji shi.

Ya kuma bayyana cewar a matsayinsu na daliban ilimin aikin jarida za su ci gaba da zagulo ababen da za su taimaki kwalejin, dalibai da kuma malamai gami da dukkanin al’umma a jiha da kasa baki daya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai