Connect with us

LABARAI

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Jiragen Yakin Helikwafta Biyu

Published

on


Shugaba Muhammadu Buhari, ya kaddamar da sabbin Jiragen yaki biyu samfurin Helikwafta Mi 35m, ranar Asabar a Kaduna, domin inganta rundunar tsaron samaniyar kasarnan.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya jiwo cewa, daga kasar Rasha ne aka sayo Jiragen a watan Afrilu.

Ministan Tsaro, Birgediya Janar Muhammad Dan-Ali, ne ya wakici Shugaba Buhari, wajen bukin kafa rundunar na 54 da ya gudana a cibiyar rundunar Sojin saman da ke Kaduna.

Buhari ya ce, an kafa rundunar Sojin saman ne a watan Afrilu na shekarar 1964 domin kammala cikar rundunar Sojin ta Nijeriya.

“Ina matsayin matashin Soja, na halarci farko har zuwa karshen yakin basasan Nijeriya, na kuma san irin rawar da rundunar sama ta taka a wancan lokacin.

‘Rundunar Sojin sama ta aiwatar abubuwa da dama na ci gaba shekarun nan, ta kuma sayo makamai kala-kala da za su taimaka mata aiwatar da aikin ta yadda ya dace.”

A cewar shi, na baya-bayan nan su ne, “Makamin, Super Mushsak, da na kwanan nan da aka kawo, Mi 35 Helicopters, da sauran makamantan sa.”

“Mun kuma rigaya mun amince da sayo Jirage samfurin, Tucano.”

Ya kara da cewa, “Samun wadannan sabbin Jiragen biyu, ya sanya ya zama wajiibi a koyar da wadanda za su yi aiki da su domin su fahimci yanda za su yi aikin da su.”

Shugaba Buhari, kuma ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu da suka wuce rundunar Sojin ta sama ta dauka gami da horar da sama da Soji 5000 domin ta inganta aikin na ta, wanda hakan kuma ya samar da ayyukan yi ga matasa.

“Ina son na kara yaba wa zaratan Sojin mu maza da mata da ma sauran sassan Jami’an tsaro kan kokarin da suka yi na fatattakan mayakan ‘yan ta’addan Boko Haram.”

Shugaban kuma ya yaba wa Kwamandojin rundunar ta sama kan aiwatar da ayyukan su kamar yadda ya dace.

Tun da farko, babban Kwamandan  rundunar Sojin saman, Iya Mashal Sadik Abubakar, ya ce, rundunar Sojin ta sama ta sami bumkasa tun hawan wannan gwamnatin.

Kwamandan Sojin saman ya ce, an sami gyara Jiragen yakin rundunar 12 da a baya suka lalace, an kuma kara karfafa zaratan rundunar da kurata 7,5000 da kuma jami’ai 400.

An kuma kafa sabbin rundunoni biyu da kuma sabbin rassa biyu, an kuma sayo sabbin makamai kala daban-daban, domin tunkarar matsalar tsaron da muke fuskanta.

“Mun kuma kafa wasu daga cikin jami’an mu a Karamar Hukumar Zurmi, ta Jihar Zamfara, su na aiki tare da sauran sassan tsaro domin magance matsalar tsaron da ke addaban yankin. Ya zuwa sati na gaba za mu tura wata rundunar zuwa garin Nguroje, na Jihar Taraba.

“A yanzun haka kuma muna gab da kammala shirin samar da kayan aiki a, Keran, ta Jihar Flatau, Ipetu Ijesha ta Jihar Osun, Doma ta Jihar Nasarawa da kuma Agatu a Jihar Benuwe.

 


Advertisement
Click to comment

labarai