Connect with us

LABARAI

Harkar Magungunan Gargajiya Na Bunkasa A Jihar Kano -Sahabi

Published

on


Masu sana’ar magugunan gargajiya dake jihar Kano , na matukar samun ci gaba  da goyon baya daga gwamnatin jihar a karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje idan ka kwatanta da shekarun baya.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban cibiyar warkar da cututtuka ta Sahabi Integrated Alternatibe Medicine Centre, dake unguwar Gwamaja a Kano, Malam Sahabi Abubakar a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanakin baya à ofishinsa.

Malam Sahabi Abubakar ya ce, samar da kasuwa ta musamman da Gwamnan na Kano ya yi ga masu sana’ar maganin gargajiyar a Unguwar Tudun Murtala a karamar hukumarn Nassarawa babbar nasara ce ga duk mai wannan sana’a, har ila yau ya kuma ce dubu 12,000 ne kacal za a rinka amsa duk shekara à matsayin kudin haya.

Wani abu kuma da gwamnan ya sake yi wa kungiyar ita ce inda ya nada mai ba shi shawara na musamman a kan magungunan gargajiya, tare da samar da ofishi domin kungiyar. zuwan gwamnan ya yi kkokari wajen hada kan daukacin masu wannna sana’a a jihar Kano.Sabodahaka su masu wannan sana’a babu abin da za su cewa gwamna Ganduje sai godiya da farin ciki.

Shugaban cibiyar da yake warkar da cututtukar da suka hada da ciyon siga, sikila da shanyewar barin jiki da cutar daji ta hanyar bayar da maganin gargajiya ya yi kira ga sauran gwamnonin kasar nan da su yi koyi da gwamnan Ganduje wajen bunkasa harkokin kiyon lafiya da kuma taimakawa masu sana’ar magungunan gargajiya a jihohin su.

Sai ya sake yin kira ga masu wannan sana’a da su sanya tsoron Allah da kuma kwatanta gaskiya a duk lokacin da marasa lafiya suka zo wajen su neman magani ko duba lafiyarsu, domin shi maganin gargajiya yana da matukar tarihi.

Da yake tsokaci game da cibiyar shi dake warkar da marasa lafiya da ba da magunguna dake Kano ya ce, ba bu shakka kara samun yawaitar mutane da suke zuwa domin duba lafiyarsu haka ya sa yake tunanin kara samar da wasu wuraren a wasu unguwannin jihar Kano da yardar Allah, domin a cewar shi yana samar da aikin yi ga al’ummar jihar tare kuma habbaka tattalin arzikin jihar da kasa baki daya .

Daga karshe ya yi addu’ar Allah ya baiwa jihar Kano da kasa baki daya zaman lafiya da karuwar arziki, sannan kuma zai ci gaba da samar da irin wannan cibiyoyi kula da lafiyar al’umma a sauran jihohin kasar nan ban da wadanda yake da su a jihohin Taraba, da Adamawa da jihar Kano da yardar.


Advertisement
Click to comment

labarai