Connect with us

LABARAI

An Yi Jana’izar Babban Limamin Katsina

Published

on


Dubun dubatar jama’a ne suka halarci jana’izar babban limamin masallacin Katsina liman Muhammadu Lawal wanda Allah Ya yi wa rasuwa bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Liman Muhammadu Lawal Dan shekaru 95 ya rasu jiya lahadi da asuba a gidansa da ke unguwar Liman cikin birnin Katsina, ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya ‘ya 70 amma yanzu 28 ne ke raye da jikoki da dama.

Haka kuma liman Malam Lawal kamar yadda ake kiransa ya shafe shekaru 38 yana jan ragamar limancin babban masallacin Katsina (wato Masallacin Sarki) da ke cikin binin Katsina a matsayin liman.

Sallar wanda aka yi ta da misalin karfe hudu na yamma jiya lahadi a filin kangiwa wanda kuma Liman Gambo Ratibi ya jagoranta ta samu halartar dubban jama’a daga cikin da wajen jihar Katsina.

 

Daga bisani kuma aka raka gawar baban limamin zuwa makwancinsa da ke makabartar Dantakun da ke cikin binin Katsina. Yanzu haka jama’a daga kowane bangare na garin Katsina suna ta tururwa zuwa zuwa yin ta’aziyar liman Malam Lawal.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan jana’iza sun hada da Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da mataimakinsa Mannir Yakubu.

Sauran sun hada da babban dan kasuwan nan Alhaji Dahiru Bara’au Mangal da shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Shitu S. Shitu da Sakataran gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammed Inuwa da kwamishinoni da ma su bada shawara da hakimai da magaddai da masu unguwanni.

A wani labarin kuma gwamnan jihar Katsina Aminu Bello MAsari ya yi ta’aziyar rasuwar liman, Malam Lawal Katsina inda ya bayyana shi a matsayin wani babban rashin da jihar Katsina ta yi, ya kuma ce liman mutun ne mai saukin kai da girmama jama’a abin koyi.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata takarda da mai taimakawa gwamna Masari ta fuskar yada labarai Abdu Labaran Malumfashi ya sanyawa hannu sannan ya rabawa manema labarai ciki har da LEADERSHIPA Yau.

Haka kuma gwamna ya yi ta’aziya ga mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da jama’ar jihar Katsina sakamakon wannan babbar rashi da aka yi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai