Connect with us

LABARAI

2019:  Abdussalam Abubakar Ya Roki Jam’iyyu Da Su Rungumi Zaman Lafiya

Published

on


Tsohon Shugaban kasannan, Janar Abdussalam Abubakar, ya shawarci ‘yan Nijeriya da kuma dukkanin Jam’iyyun siyasar kasarnan, da su shelanta zaman lafiya a cikin dukkanin shirye-shiryen su na tunkarar zabukan 2019.

Tsohon Shugaban, ya bayar da wannan shawarar ce sa’ilin da yake tarban ‘ya’yan kungiyar Shugabannin Arewa da kuma na kungiyar majalisar masu ruwa da tsaki, (NSLA) da suka kai ma shi ziyara a gidan sa da ke Abuja, ranar Asabar.

Abdussalam, ya ce, “Matukar ba zaman lafiya, to kasar ma ba ta kenan, in ba zaman lafiya, to siyasar ma ba ta.

“Don haka ya zama tilas ga kowannen mu ya bayar da na shi gudmmawar wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin kasarnan.

“Duk wadannan kashe-kashen na rashin imani da manyan munanan ayyukan da ake aikatawa ba inda za su kai mu. Don Allah, mu hada hannu mu samar da zaman lafiya.”

Ya ce, da zaran mutane sun samar da zaman lafiya, tabbas za su iya warware duk wata matsalar da ta taso a tsakanin su.

Kan shawarar da ya baiwa gwamnati na ta yi kokari ta shawo kan matsalar yawaitan kashe-kashe a sassan kasarnan, ya shaidawa manema labarai cewa, kowa ma yana da gudummawar da zai iya bayar wa wajen magance matsalar ta tsaro.

“Duk masu aikata wadannan laifukan, ‘yan Nijeriya ne ko kuwa daga waje ne suke shigowa kasarnan suna aikata barnan. Mun taba kawo rahoton ga su nan suna shigo mana kasa? Muna bayar da bayanan sirri a kansu?

“In kuma ‘yan Nijeriya ne, ashe ba yayyinmu da kannanmu ne ba? Ba mu san su ne ba? Mun taba tona masu asiri? Don haka kowa yana da gudummawar da zai iya bayar wa.”

Ya kuma shawarci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da rokon Allah kan ya tausaya mana ya kuma magance mana wadannan lamurra da ke addaban mu, domin a samu zaman lafiya.

Shugaban tawagar, Alhaji Tanko Yakasai, ya shaidawa manema labarai cewa, sun kawo ziyarar ce domin su sanar da tsohon Shugaban kasan kasantuwan kungiyar su kuma nemi goyon bayan sa.

Yakasai ya ce, kungiyar na su ba ta siyasa ce ba, amma dai za ta rika tattauna lamurran siyasa domin samar da mafita da kuma makomar kasarnan.

Ya kuma ce, ba abin da ya hada kungiyar da zaben 2019.

“Kowa yana da daman goyon bayan duk wanda ya ga dama, yana kuma iya shiga duk Jam’iyyar da yake so.


Advertisement
Click to comment

labarai