Connect with us

LABARAI

Rudani Ya Dabaibaye Zaben Wakilan APC A Kebbi

Published

on


 

Shugaban Kwamitin gudanar da zaben mazabun unguwanni da kuma na kananan hukumomi sanata Alkali Lawal Jajere ya bayyana wa manema labaru a Birnin-kebbi a jiya cewa “ kananan hukumomi 18 a cikin 21 da ke a jihar ta kebbi sun sasanta amma kananan hukumomi uku kamar Bagudo, Suru da kuma koko-Besse basu iya sasanta wa ba har a jiyan da ake batun gudanar da zaben wakilan mazabun unguwanni a jihar “. Sanata Alakali Jajere ya ci gaba da cewa “ akwai matsalar da ake fuskanta a zaben na mazabun unguwanni shine wasu ‘yan takara sun biya kudin takardun takarar amma basu samu takardun ba, amma Kwamitin gudanar da zaben a karkashin jagorancinsa ya baiwa ‘yan takarar takardun nasu domin su samu damar tsayawa takara a mazabunsu”. Haka kuma yace “ lakacin da aka sanya na fara gudanar da zaben shine daga karfe takwas na safe zuwa karfe biyar na yamma, amma tun da an samu bacin lokaci zuwa mukara lokaci har zuwa karfe bakwa na yamma kafin kammala karbar sakamakon zaben na mazabun unguwanni a duk fadin jihar ta kebbi “.

Su ma wasu ‘yan jam’iyyar APC ta jihar kebbi sun karyata maganar da shugaban Kwamitin gudanar da zaben mazabun unguwanni Sanata Alkali Lawal Jajere ya sanar ga manema labaru a jiya a Birnin-kebbi, da ya ke bayyana wa manema labaru a Birnin-kebbi a jiya jin kadan bayan shugaban Kwamitin ya kammala jawabansa ga ‘yan jarida, Barista Aminu Shamaki ya bayyana wa LEADERSHIP A Yau Lahadi yace “ maganar da shugaban Kwamitin gudanar da zabe sanata Alkali Jajere yafadawa manema labaru a jiya a Birnin-kebbi cewa an sasanta tsakanin ‘yan takara na kananan hukumomi 18 a cikin 21 da ke akwai a cikin jihar ta kebbi sun sasanta junnan su cewa kananan hukumomi uku ne kawai anba su sasanta ba , wannan bayanin ba gaskiya bane domin mutane na mazabunsu tun da safe suna jiran a zo a gudanar da zabe amma ko takardun tsayawa takara da wasu ‘yan takara suka saye ba a basu ba balle a ce an sasanta”. Saboda haka Batista Aminu Shamaki ya ci gaba da cewa “ wannan ba damokaradiyya bane sannan uwar jam’iyya ta APC ta sanda cewa ba’a yi a gudanar da zaben mazabun unguwanni ba a jihar kebbi saboda mutane nason su zabi mutanen da sukeso amma ba’a basu damar yin hakan ba”.

Shi ma wani dan jam’iyyar ta APC daga karamar hukumar mulki ta Jega Alhaji Junaidu Haruna jega ya bayyana wa wakilin LEADERSHIP A Yaulahadi yace “ basu gansu da maganganun da shugaban Kwamitin gudanar da zaben wakilan mazabun unguwanni ya fada ba domin babu inda aka cinma matsaya tsakanin ‘yan takara ba, kuma jama’a sun fito a mazabunsu tun da safe suna jiran masu gudanar da zabe suzo amma babu wanda yazo “. Saboda haka” muna kari ga uwar jam’iyya ta kasa da kuma masu ruwa da tsaki da susani cewa ba’a gudanar da zabe ba”.


Advertisement
Click to comment

labarai