Connect with us

LABARAI

Rasuwar Yayar Sule Lamido Ta Girgiza Shi

Published

on


Rasuwar Hajiya Yahanasu lamido Dattijuwa mai shekaru 86 A Duniya, Yaya Yar’uwa ga tsohon Gwamnar Jahar Jigawa Alhaji Sule Lamido wannan Rashi ya girgiza Daukacen iyalai da zuriyar Alhaji Sule Lamido kasancewar Hajiya yahanasu I ta ce babba da ta rage a cikin zuriyar Sule Lamido, kamar dai yadda dan uwa kuma auta a dakin su Sule Lamido watu Bello Lamido ya baiyana ya ce wannan babban rashine a garesu musaman a matsayin ta na Yayarsu kuma wacce ta ke amatsayin uwa kaka agaresu abine da girgizasu kuma tabar gibi a tsakaninsu mai wuyar cikiwa dan haka dan haka ba abincewa sai dai Allah yagafartamata ya Sa Aljanna makuma.

Shi ma Alhaji Mustapha Sule Lamido wanda da ne ga Hajiya yahanasu kasancewar ta Yaya ga Sule Lamido ya ce a matsayin ta na baya mai goya marayu abu ne da yasa dole abubuwanda basu sani ba na daukar nauyin baki nata da nasu da ma wand aba a saniba duk aikin ta ne to kuma yanzu bata to wannan yadawo kansu don haka dole susake damara wajen sadarda zumunci a wannan zuria tunda nauyi yadawo kansu wanda da ita take taimaka musu wajen daukar wannan nauyi dan haka yanemi yan uwa da masoya suyi hakuri rashinta da kuma yin Addu’a gare ta da sauran musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.

Rahotanni daga Bamaina mahaifar Alhaji Sule Lamido sun tabbatar da cewa shugabanni nada dana yazu da sauran Kungiyoyi cigaban Al’umma, mallamai yan kasuwa, yan siyasa da Daliban makarantu a matakan furamare, sakandare, da Jami’oi na tururuwa zuwa Garin Bamaina da ke maramar Birnin Kudu a Jahar Jigawa dan yiwa tsohon Gwamna Alhaji Sule Lamido Ta’aziyar Rashin Yar Uwa da yayi a ranar laraba da ta gabata.


Advertisement
Click to comment

labarai