Connect with us

ADABI

Lawan PRP Ya Zama Na Daya A Gasar ‘Ina Mafita’ Ta Marubuta Group

Published

on


Gasar ta gajeren labari da zauren marubuta ya sanya mai taken Ina Mafita? ta samu tagomashin duruwar matasan marubuta daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya. An bukaci masu yin gasar ne da su rubuta gajeren labari a kan yawaitar fyade a kasar Hausa da kuma hanyoyin magance shi.

An dai fitar da sakamakon ne da kuma karrama wadanda suka yi nasara a gasar ranar Lahadin da ta gabata (29/04/2018) a dakin taro na American Corner da ke Murtala Muhammad Library Kano.

Lawan Muhammad Prp, shi ne zakaran da ya lashe gasar a matakin farko da labarinsa mai taken Sai Bango Ya Tsage. Lawan PRP dai marubuci ne da ya jima yana gwagwarmaya a duniyar rubutu da marubuta, shi ne marubucin littafin Bakin Dare, Kwanan Gida, Matar Marubuci da dai sauransu.

Bayan rubutun zube Malam Lawan yana rubutun finafinan Hausa, yanzu haka shi ne sakataren kungiyar marubutan Hausa ta Hausa Authors Forum.

Malam Lawan Muhammad PRP, shi ne ya zo na biyu a gasar gajeren labari da Makarantar Malam Bambadiya ta shirya a shekara ta 2014.

PRP ya shaida wa wakilinmu cewa, “farko dai Ina godewa Allah da ya ba ni hikima da basirar yin rubutu, don wannan baiwa ce da Allah kan ba wa wanda ya so ba kuma don ya fi son sa a cikin bayinsa ba. To haka nasarar da na samu ita ma daga gare shi ne, don haka ba abin da zan ce face Alhamdulillah. A karshe kuma ina yabo da jinjinawa Zauren Marubuta da ya shirya wannan gasa, saboda wannan aiki ne na sadaukarwa, kuma babbar gudummawa ce ga adabin Hausa, Allah ya saka musu da alkhairi. Kuma ina fatan wannan gasa ta zama mafari, saboda shirya irin wannan gasa yana kara zaburar da marubuta matuka.”

Bilkisu Bilyaminu ce ta lashe gasar a mataki na biyu da labarinta mai taken Taimakon Kai Ya Fi Taimakon Dangi. Bilkisu matashiyar marubuciya ce sananniya acikin marubutan yanar gizo, memba ce ta kungiyar Fikira Writers Association, ita ce marubuciyar littafin Kasaitattun Mata.

King Isah Boy shi ne ya yi nasara a gasar a mataki na uku. King Isah daya ne daga cikin shugabannin kungiyar marubuta ta Zamani Writers Association, shi ne marubucin fitaccen littafin nan Feshin Jini, Aljanar Fatima, Mijin Aljana da dai sauransu. Da wakilinmu ya tambaye

shi me zai ce game da sakamakon wannan gasa, sai ya amsa da cewa “a gaskiya na yi farin ciki sosai da nasarar da na samu, kuma na yi mamaki saboda wannan shi ne karo na farko da na soma shiga gasa a fannin rubutu.”


Advertisement
Click to comment

labarai