Connect with us

LABARAI

Fintiri Ya Yi Allawadai Da Tagwayen Hare-Haren Mubi

Published

on


Tsohon mukaddashin gwamnan jihar Adamawa, Umaru Ahmadu Fintiri, ya nuna damuwa da harin bama-baman da ya sabbaba asaran rayukan jama’a da dama a garin Mubi, yace lamarin abun allawadai ne.

Wannan bayanin na kunshe cikin wata sanarwar manema labarai, da maimaka mishi kan harkokin sadarwa da hakakan jama’a Mista Steben Maduwa, tace Fintri na jajantawa ‘yan uwa da abokan jama’ar da suka rasa rayukansu a ya’yin tashin bama-baman.

Sanarwar ta ci gaba da cewa “wannan harin aiki ne na wawaye makiyan ci gaban jihar, da nuna tsananin kiyayyarsu ga wanzuwar dan adam,” ta ce.

Fintri, wanda tsohon mamba ne mai wakiltar karamar hukumar Madagali a majalisar dokokin jihar, tashin bama-baman abun kaico ne wanda ke neman kassara zaman lafiyar da’aka samu a yankin da garin Mubi.

Sanarwar ta kuma yi fatan jama’ar da suka jikkata sakamakon tashin bama-baman zasu samu sauki cikin gaggawa, ta kuma jajantawa iyalan wadanda suka mutu.

Haka kuma tsohon mukaddashin gwamnan ya jajantawa jama’ar Numan, inda wasu ‘yan bindiga sukakai hari kan wasu kauyuka uku inda aka samu asaran rayuka da dama, tace lamarin abin bakin ciki ne, ta kuma yi fatan Allah ya kawo karshen lamarin baki daya.

Haka kuma ta yaba da kokarin da gwamnatin jihar da jami’an tsaro ke yi kan lamarin tsaro a jihar, ta kuma nemi da su kara kaimi domin lamarin ya zo ga karshe.

Sanarwar ta kuma yi kira ga jama’a da su sa ido da hada hanu da jami’an tsaro domin gano masu aikata wannan danyen aiki a jihar.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai