Connect with us

LABARAI

Dalilan Da Su Ka Sa Zan Yi Takarar Majalisar Jihar Gombe –Katukan Bolari

Published

on


Wani matashin dan siyasa a jihar Gombe tsohon hadimin Uwargidan gwamnan jihar kuma tsohon Kansilar Unguwar Bolari a fadar jihar Gombe Alhaji Yusha’u Yakubu Katukan Bolari Dan Autan PDP ya bayyana dalilansa kwarara guda uku da suka sa shi yake son fitowa takarar kujerar dan majalisar tsara Dokoki na jihar Gombe da zai wakilci Gombe ta kudu a jam’iyyar su ta PDP.

Alhaji Yusha’u Yakubu Dan Autan PDP ya bayyana dalilan nasa ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a Gombe inda ya fara da cewa idan ya zama zababben dan majalisar jihar Gombe zai bai wa gwamnati shawarin cewa a dawo da irin kananan asibitocin nan irin na da na sha ka tafi da ake dasu a unguwanni wato Dispensary dan inganta harkar kiwon lafiya.

Ya ce, bayan wannan zai mika kuduri a gaban zauren majalisa na ganin cewa gwamnatin jihar Gombe ta bullo da wani tsari na samar da wani waje na musamman dan tara jini da za’a dinga taimakawa masu bukatar Karin jini da basu da hali a asibitin kwararru na jiha wato Blood bank a kuma ware wata rana da duk mai bukatar taimakawa da jini zai je a ja kamar yadda ake yi a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya FTHG.

Dan Autan PDP, ya kuma kara da cewa saboda harkar lafiya ita ce kan gaba idan aka bullo da wadannan tsare-tsare za’a samu sauki na cincirundon jama’a musamman mata marasa lafiya a asibitoci sannan a kara ingata cibiyoyin lafiya matakin farko Primary health centers dake fadin jihar dan ko haihuwa Mace taje a lokacin da ya kamata a karbeta da wuri saboda yawan jama’a akan samu matsala.

Ya kara da cewa tunda dan majalisa baya bada kwangila zai hada kai da sauran mambobin majalisar da suka fito daga mazabu daban daban wajen neman goyon bayan su dan a dinga kawowa mazabar sa abubuwa na ci gaban rayuwa da suka dace.

Har ila yau Dan Autan PDP a cewar sa kasancewar sa dan siyasa tun daga tushe kuma dan jam’iyyar da take mulki a Gombe wato jam’iyyar PDP baya jin cewa zai samu matsala a wannan kuduri nasa domin a shekarar 2019 yana hango cewa da yardar Allah babu wani dan jam’iyyar APC da zai ci zabe majalisa za’ayi ta yan PDP zalla kai ko wani dan wata jam’iyya ma yaci zabe ba zai zama musu barazana ba so ne ke da rinjayen majalisa.

Ya yi amfani da wannan damar inda ya shawarci gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, da cewa ya goya wa ‘ya’yan jam’iyyar sa ta PDP baya tun daga kan dan takarar kansila har zuwa kololuwa dan ganin ba’a fadi a zabe ba saboda idan suka ci zabe suyi koyi da irin ayyukansa kyawawa da ya yiwa al’ummar jihar Gombe.

Da ya ke mazabun nasa Bolari da Kumbiya-Kumbiya da Pantami da Jekadafari ne yace zai duba kowacce unguwa ya ga menene matsalar su ya kwatanta yi musu wani abu da zai ciyar da unguwar gaba amma duk hakan ba zai yiwu ba sai jama’ar yankin sun ba shi goyon baya sun kada masa kuri’a a wanann zabe dake tafe na 2019 bayan ya kada kowa a zaben fitar da gwani.

Daga nan sai Alhaji Yusha’u Yakubu Dan Autan PDP, ya yi kira ga matasa yan uwansa da dattawa da cewa kowa ya fita ya yanki kuri’a domin duk yadda kake son mutum yaci zabe muddin baka da katin zabe da zaka zabe shi ya zama aikin banza dan haka su tashi su nemi kuri’a domin ita kuri’ar ita ce ’yancinsu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai