Connect with us

LABARAI

An Kashe Dan Takarar Shugaban APC A Delta

Published

on


Wani dan takarar kujerar shugaban jam’iyyar APC na Gundunama ta 10 (Jeremiah III) da ke karamar hukumar Ughelli a jihar Delta mai suna Mr Jeremiah Oghobeta, ya gamu da alajinsa a sakamakon wani farmakin da wasu ‘ya’yan jam’iyyarsu wanda har zuwa yanzu ba a kai ga gano ko su waye ba suka hallaka a jiya Asabar.

Kisan nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke tsaka da gudanar da zaben shugabanin APC a matakan Gundumomin jihar da sauran sassan kasar nan.

Wata majiyarmu ta shaida mana cewar, hatsarin ta auku masa ne a lokacin da suke tsada da jiran a kawo musu kayayyakin gudanar da zaben daga jagororin gudanar da zaben masu kula da wannan jihar, an samu artabu sosai a lokacin da ake gabatar da jerin sunayen wadanda za su tsaya neman sa’arsu daga bisa dai aka kai masa wannan harin da ta kaisa ga bakwantar lahira.

Kawo yanzu dai zaben jam’iyyar na ci gaba da gudunawa, inda a halin da ake ciki wasu ke korafin yadda zaben ke gudanuwa da sauransu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai