Connect with us

LABARAI

Za A Gudanar Da Zaben Shugabanin NUJ A Neja

Published

on


An yi kira ga mambobin kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Neja da suka cika ka’idar jefa kuri’a da su tabbatar sun fito dan jefa kuri’arsu ga shugabannin da zasu jagoranci kungiyar na wasu wa’adin shekaru uku masu zuwa. Shugaban Kwamitin zaben, Alhaji Usman Chiji ne yayi kira a lokacin da yake zantawa da wakilin mu.

Usman Chiji yace dukkan sassan kungiyar da ke jihar kowa zai jefa kuri’a kamar yadda doka ta tsara, yace duk wani abu da zamu a lokacin zaben nan zamu bi dokokin kungiya ba zamu saki layi ba, dan haka duk dan kungiya da ya cika ka’idar kungiya na da damar jefa kuri’a kuma kowani shugaban sashe ya tabbatar ta ka kunnen mambobinsa na ganin ba su kaucewa dokokin kungiya ba.

Zaben dai za a yi shi ranar littinin 30/04/18 a sakatariyar jam’iyyar da ke IBB Pen House a cikin garin minna.

Kujerar da tafi daukar hankali ita ce kujerar shugaba na jiha wanda za a kara tsakanin Kwamred Muhammed Muhammed ( Sa’in Gunna) wanda ke neman zango na biyu, ma’aikacin kamfanin jaridun gwamnatin jiha, Newsline Newspapers, da kuma tsohon sakataren kungiyar na jiha da ya taba nema matsayin a baya Abdul Idris na gidan radiyon jiha, zaben dai ana sa ran fara shi da misalin takwas na safe.

 


Advertisement
Click to comment

labarai