Connect with us

LABARAI

’Yar Fim Ta Karyata Yi Wa Atiku Martani

Published

on


Shahararriyar ‘yar fim din Hausa. Rahama Sadau ta fitar da kakkausar martani ga rade-radin dake yawo da shi a kafafen sadarwa na cewa ta soki tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Jita-jitar da ake yawo da ita ta bayyana cewa, wai jarumar ta soki Alhaji Atiku Abubakar ne saboda martanin da ya mayarwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kalaman da yayi na kiran matasan Nijeriya da ci-ma zaune.

Jarumar ta ce; “Ina so na karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa na caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan martanin da ya mayar wa Shugaba Muhammad Buhari na cewa matasan Nijeriya ’yan cima zaune ne.

Ba ni da wata jam’iyya, ban kuma zabi wani dan takara ba, ba na kuma wata kungiya da ta jibanci siyasa ko cikin wata tafiya ta siyasa. Ina so in sanar da mutane cewa ban yi hira da wata kafar yada labarai ba dangane da labarin da ake yadawa. Babu wani abu na labarin da ake yadawa da yake gaskiya.” inji ta

ta kara da cewa; “Ina kira ga al’umma cewa kada su yarda da labarin da suka gani ana yadawa, sannan ina gargadin wadanda suka kirkiro labaran da su daina bata mun suna. Ina kira ga kafafen yada labarai da su tsaya a kan aikinsu kamar yadda ka’idojin aikin jarida ya shimfida, sannan duk wani abu da suka gani an alakanta shi da ni, to su rika tuntuba ta don su tabbatar da sahihancinsa ko akasin hakan.”

 


Advertisement
Click to comment

labarai