Connect with us

LABARAI

Sanata Hunkuyi Ya Tsallake Rijiya Da Baya 

Published

on


“Yan bangar siyasa fiye da 20 dauke da muggan makamai ne suka kai wani munmunan hari taron gangamin siyasa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na yankin mazabar majalisar datijjai ta tsakiya a jihar Kaduna suka kira, inda dan majalisar datijjai mai wakilar Kaduna ta tsakiya a majalisar kasa Alhaji Sukeiman Usman Hunkuyi ya tsallake rijiya da baya inda ‘yan bangan dauke da muggan makamai suka jikkata mutane da dama.

Sanata Suleiman Hunkuyi ya bayyana cewar, ‘yan bangan sun dira wajen taron ne dauke da muggan makamai daban daban in da suka shiga sarar duk wanda suka gani abin daya kai ga jikkata mutane da dama tare da lallata motoci da dama.

Bayanin ya ci gaba da nuna cewar, an garzaya da  wadanda suka ji ciwo asibitin Garkuwa da asibitin Barau Dikko duk a cikin garin Kaduna domin yi musu magani.

Cikin motocin da aka farfasa har da na shugaban kanfanin ATAR Communication” masu gidan Talabijin da Radio na Liberty Alhaji Tijjani Ramalan. A na gudanar da taron ne a dakin taro na NUC, unguwar Mogadishu layout, Yan Doya, Kaduna.

Idan za a iya tunawa, kusan irin wannan lamarin ya faru a cikin shekarar data gabata inda ‘yan banga suka mamaye cibiyar ‘yan jarida NUJ ta jihar Kaduna inda Sanata Suleiman hunkuyi da sauran wasu ‘yan majalisa suke ganawa da ‘yan jarida inda suka ji wa mutane da dama ciwo suka kuma hargitsa taron manema labaran.

Sanata Hunkuyi ya yi tir da harin da aka kawo, ya kuma ce, lallai wadanda suke fargabar irin karbuwar daya ke samu ne a fagen siyasa suka kitsa, ya kuma tabbatar musu cewa, ba za suyi nasara ba.

Ya zuwa hada wannan rahoto, rundunar ‘yansandan jihar Kaduna basu fito da wani jawabi a kan harin da aka kai ba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai