Connect with us

LABARAI

Rashin Adalci Ne Ke Sa Ake Cewa Matasa Sun Kasa –Yahaya

Published

on


An jawo hankalin majalisar dattijai da ta wakilai akan kar su yarda su jawo abinda zai mayar da siyasar kasar nan baya, domin kokarin zartar da wani abu wanda ya sabawa dokokin kasar nan kuskure ne babba. Mawallafin jaridar Nigerwich, Yahaya Muhammed Usman ne ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin da yake tsokaci kan yunkurin majalisar dattijai na tsige shugaban kasa kan zargin yin gaban kansa wajen bada aiki na makuddan miliyoyi wanda suka ce ba a tuntubi majalisar ba a lokacin fitar da wadannan miliyoyin kudi, wanda hakan suka ce ya sabawa dokokin kasar nan.

Malam Yahaya yace idan abinda majalisar ke zargi ya zama gaskiya to lallai fadar shugaban kasa ta tabka babban kuskure, domin kwanakin baya majalisa ta zargi fadar da fitar da wasu kudaden wanda komai muhimmancin abin indai za a bi doka yafi rashin bin dokar muhimmanci. Shugaba ya ta ka doka yafi zama illa akan cewar talaka ne ya taka dokar, amma yau kasar nan ta zama doka ba ta aiki akan kowa sai talakan kasa, mai mulki zai iya yin abinda ya ga dama kuma ya sha.

Amma duk da hakan ya kamata kafin daukar kowani mataki daga bangaren majalisar ta tabbatar tayi bincike na hakika da kuma bin bahasi kamar yadda dokokin kasa suka tsara, amma gaskiya a irin tafiyar da ake akwai hadari babba.

Da ya juya kan zargin da ake wa matasa na kasa wa bisa jagoranci kuwa, yace a gaskiya akwai rashin adalci, dan an gwada Goodluck Jonathan ya kasa ba shi zai sa a debe tsammani ga matasa ba, domin a kasar matasa ne akan gaba da komai, idan ka je aikin soja matasa ne kan gaba, idan ka je aikin ‘yan sanda matasa kan gaba, idan ka tafi kwatsam da duk wani aikin kare kasa matasa ne za ka gani ka gaba, a lokacin da aka zo maganar shugabanci sai a rika tauye matasa, wanda wannan zalunci ne babba.

Idan ka duba Yakubu Gowan yana da shekaru na wa ya mulkin kasar nan, sannan ka dubi Obasanjo yana da shekaru na wa ya mulki kasar nan, kai duk wani da ya nuna jarunta a kasar nan yana da shekaru na wa a rayuwarsa ya samu wannan matsayin, in ko haka ban ga dalilin da zai sa kullun a rika tauye matasa ban da bangar siyasa da tura su miyagun abubuwa da ake yi sannan a dawo a toshe masu gurabunsu da hana su inganta tunaninsu wanda wannan kuskure ne babba.

Ya zama wajibi matasa mu fito takarar mukaman siyasa na dukkanin mukaman da aka tsayar kuma aka amince da su, domin mu din dai ne ma su yiwa tsoffin aiki ko, to gara mu hada kai mu yiwa junan mu domin mune muka san darajar junan mu. Amma ba adalci ba ne abinda ake wa matasa, an mayar da mu gugar yasa, wanda ba zamu lamunci hakan ba. Ba zamu sa ke bata lokacin mu akan tallata kowani makiyin matasa ba, ya isa haka, ya kamata a ja layi haka nan.

Duk wani kujerar siyasa matasa mu fito kwan mu da kwarkwata mu marawa juna, domin duk lalacewa na ka dai na ka ne duk tsiya matashi ya san darajar dan uwansa matashi yasan matsalolin da ke damun ‘yan uwansa ban ga dalilin da zai sa a ce kullun matasa mu aka mayar cima zaune, mu aka mayar wadanda ba su san kimar Kansu ba.

Saboda haka 2019 kakar siyasar matasa ne a kasar nan, daga kujerar kansila har shugaban kasa zamu nema, yanzu ya kamata dattawan nan su koma gefe su zama masu bada shawara, domin kasashen da aka cigaba in ka lura dattijai sun taka rawar su a harkokin mulki yanzu sun koma baya sun zama masu bada shawara kuma ka ga suna samun cigaba sosai.

Maganar bangar siyasa da shaye- shaye da matasan mu suka samu kansu a yau da gangan ake jefa su dan son zuciya, wanda kuma ba wani shiri da aka yi na ganin an fitar da su, to lokaci yayi da mu da kan mu zamu yaki bangar siyasa da zaman rashin aiki dan ceto rayuwar mu daga wannan mummunar halin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai