Connect with us

LABARAI

Obasanjo Da Babangida Na Yakar Buhari Ne Saboda Ya Na Yaki Da Rashawa —Ganduje

Published

on


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce, tsaffin sguhabannin kasar nan, Olusegun Obasanjo da Ibrahim Babangida, na yakar sake neman zaben da shugaba Muhammadu Buhari keyi ne saboda hankoron wannnan gwamnati na magance annobar cin hanci da rashawa dukkan fannonin rayuwar ‘yan Nijeriya.

Ganduje ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da jaridar PUNCH, inda ya ce, Obasanjo da Babangida da sauransu da ke kalubalantar shugaban kasa basu da wani mutuncin yin haka.

Ya zargi Obasanjo, da kokarin haifar da rikicin tsarin mulki a lokacin da ya yi kokarin amfani da majalisar kasa don zarcewa a matsayin shugaban kasa har na shekara 8.

Ganduje ya kuma ce, “Ku dubi Obasanjo da kuma lokacin da yake kokarin yin tazarce a karo na uku, ko ka san ko nawa aka kashe a hankoronsa na yin tazarce? An kashe biliyoyin Nairori, shin dole sai an jirkita tsarin mulki don kawai kana son zama shugaban kasa? Iri wadannan mutanen ne zasu mukemu?

Ya kuma nuna mamakinsa yadda mutum kamar Babangida, da aka kora da karfi daga kan karagar mulki bayan ya ki mika muki ga wanda ya lashe zabe, a zaben da aka gudanar ba tare da wani magudiba, har shi ne ke da karfin halin cewa, shugaba Buhari kada ya tsaya takara a karo na biyu.

Ya kuma saba da ra’ayoyin tsaffin janarorin na cewa Buhari ya kasa samar da tsaro a sassan kasar nan ya kuma kasa tayar da komatsan tattalin arzikin kasa.

Ya kara tabbatar da cewa, matsalarsu da gwamnatin Buhari a halin yanzu shi ne kudirinsa na ci gaba fatattakar masu cin hanci da rashawa a fadin tarayyar kasar nan.

“Mu kara duba abin daya shafi tsaffin shugabanin kasar nan guda biyu, Ibrahim Babangida ya mulki kasar nan na tsawon shekara 9 daga karshe ya ki barin karagar mulki, daga karshe aka gudanar da zaben shugaban kasa, aka kuma zabi shugaba amma ya soke zaben ba tare da wani dalili ba”

“Shin Muhammadu Buhari ya yi irin wannan laifin a siyasance? Babangida ya so ya yi tazarce amma ya kasa sai ya kirkiro da gwamnatin rikon kwarya, amma da sharadin zai sake dawo wa kan karagar mulki.

“Mutumin da ya yi mulki na tsawon shekara 9, yana kuma hankoron ci gaba da mulki ko ta wane hali yana kuma kokarin hana wani da ya yi mulki na shekara 4 kuma ga shi tsarin mulki ya ba shi daman sake neman takarar na wasu karin shekara 4 a mulkin Nijeriya.

Gwamnan Kanon ya kuma kara da cewa, “A saboda haka Obasanjo da Babangida basu da mutuncin da zasu ba Buhari shawarar cewar, ya yi wa’adin mulki daya, saboda haka babu wanda zai dauki shawarwarin da suke bayawa da wani mahimmanci.

“Wadanda suke yaki da Buhari suna yi ne saboda yana yakan cin hanci da rashawa ne, amma jama’ar kasa na tsananin farin ciki da yaki da cin hanci da rashawan da shufaba Buhari yake yi, shi yasa muke bukatar shugaban kasa ya sake takara a zaben shugaban kasa na shekarar 2019”

Gwamna Ganduje ya ce, kwamnoni da dama ne suka matsa wa shugaba Buhari ya fito takaran shugabancin kasa, kafin ya amince, ya fito takarar shugabancin kasa.

Ya lura da cewa, tun da shugaba Buhari ya cika dukkan alkawuran da ya yi wa jama’a a yayin yakin neman zabe, lallai ya kamata ya sake neman shugabanci a karo na biyu.

Da aka tambaye shi, kokarin da suka yin a ganin shugaban kasa ya sake neman zabe a karo na biyu, Ganduje ya ce, “wasu daga cikin gwamnoni sun dade suna lallashin shugaba Buhari ya sake neman takara wa’adi na biyu musamman ganin Shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya ya kuma yi imani da tsarin mulkin kasa da bukatar bin tanade tanaden ta sau da kafa”

“Ya tabbatar da zai inganta harkar tsaro a cikin kasa zai kuma yi maganin ‘yan ta’adda tare da farfado da tattalin arzikin kasa”.

“Wadannan lamurorin nada matukar mahimmanci, shi ya sa nake ce maka Buhari zai lashe zaben shekarar 2019 da kuri’u fiye da abin daya samu a shekarar 2015”.

 


Advertisement
Click to comment

labarai