Connect with us

LABARAI

Kwalejin Ilimi Ta Jihar Jigawa Ta Dauki Sabbin Dalibai 290

Published

on


Kwalejin ta jihar Jigawa dake garin Gumel ta sanar da daukan dalibai 290 a zangon karatu na wannan shekarar na 2017/2018.Wadanda aka dauka sun fito ne daga bangarorin darussan Biology da Chemistry da kuma Agri, sai kuma sauran da suka hada da bangaren Hausa islamic Studies da English Language.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin mataimakin shugaban tsangayar ilimi na Digiri dake makarantar Dr. Yahya Sani a lokacin da yake zantawa da manema labarai a makarantar kwanakin baya.

Dakta Yahya Sani, ya kara da cewa nan gaba kadan za a gudanar da bikin rantsar da daliban a harabar makarantar, ya ce, matukar aka ci jarabawa da kula da jami’oi ta kasa ke shiryawa za ta kara ba da damar karin wasu kwasakwasan.

Shaidar da suke bayarwa na kammala kwalejin yana fiowa daga jami’ar Bayero dake Kano watau BUK su shaidar da suke bayarwa ta NCE ne kawai. Mataimakin tsangayar ilimin ya nuna farin ciki game da yadda makarantar ke kara samun ci gaba da kuma bukasa inda suka samu yaye dalibai wanda BUK ta ba su shaidar kammala makarantar kimanin 64.

Duk da makarantar an samar da ita ne domin al’ummar jihar Jigawa amma a kan ba da guraben karo karatu ga wasu al’ummar jihohin kamar Kano da Katsina da Yobe , da sauran su.Wani abin sha’awa shi ne makarantar tana da malamai masu hazaka da mayar da hankali a kan abin da suke yi, suma daliban suna da hazaka wajen mayar da hankali akan abin da ake koya masu.

Kwalejin na tura malamai karo karatu a wasu manyan jami’oin kasar nan har da na kasar waje, sai ya yi amfani da wannan dama da kira ga daliban dake karatu da su kara himmar da aka san su da shi a kan karatu da kuma tarbiyar koyarwar addinin musulunci.

Ya kuma gode wa Allah game da yadda ake samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin malamai da daliban makarantar, musamma yadda tun tarihin makarantar ba a taba samun kungiyoyin asiri ba wannan abin nuna farin ciki ne ga Allah.

Shi ma mai rikon rajistarar na makarantar Malam Muhammad Ahmad Haruna, ya gode wa shugaban makarantar a kan kokarin ciyar da makarantar gaba tare da gudanar da shugabanci tsakani ga Allah, tare da gudanar da aikace aikace masu muhimmanci a daukacin makarantar.

Haka kuma mai rikon rajistaran ya ce, albashin malamai da ma’aikatan makarantar ana ba su a kan lokaci ba tare da jinkiriba wannan na daya daga cikin abin dake sa ake kara kwazo a wurin aiki ba tare da ha’inci ba, shi ma ya gode wa Alla da zaman lafiya tsakanin malamai da dalibai sai ya yi addu’ar Allah ya kara bayar da zaman lafiya a makarantar da jihar Jigawa da kasa baki daya.


Advertisement
Click to comment

labarai