Connect with us

LABARAI

An Yi Wa Noma Kyakyawan Tanadi A Daminan Bana

Published

on


Ganin yadda daminan bana ta fara kankama a wasu wuraren, ya sa babban dilar sayar da magungunan kwari da da irin shukawa na kamafanin Amarshal agro tech Alhaji Tijjani Umar Tinau Malikawa Garu, ya yi wa manoman kasar nan kaykkyawan tanadi domin gamsar da manya da manoman kasar nan.

Tijjani Umar Tinau, ya shaida wa manema labarai kwanakin baya a Kano, ya kara da cewa, kayayyakin da za su saidawa manoman za su same shi cikin sauki da rahusa ta yadda mai karamin karfi zai iya sanyawa a gonarsa.

Cikin kayayyakin da suka tanadar wa manoman a bana har da takin zamani amma na ruwa wanda Amarshal ya samar da shi, abin mamaki shi ne wurin da manomi yake samun buhu biyu na anfanin gona idan ya sanya takin na ruwa zai iya samun buhuna uku zuwa hudu.

Malikawa Garu ya ce, manoma sun yi amfanin da wannan sabon sinadarin na taki sun tabbatar da haka, yana kuma da inganci.

Matashin dankasuwan da yi suna wajen taimakawa marasa karfi da kuma yake gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar sabon garin Kano, ya ce, babu shakka takin yana da sauki ga manoma idan ka kwatantashi da takin da aka sani.

Ya yi amfani da wannan dama da kira ga al’umma da cewa su rungumi shirin nan na shugaban kasa na cewa a koma gona domin ciyar da abinci ga kasa maimakon shigo da shi. Sannan ita kuma gwamnati data taimakawa manya da kananan kungiyoyin manoma da kayan aikin gona irin su taki da irin shukawa da kuma magungunan kwari da kuma tantan na noma.

Alhaji Tijjani Umar Tinau, ya godewa Amarshal a kan taimaka wa harkokin noma a kasar nan musamman magungunan kwari da kuma irin shukawa da taki na ruwa masu kyau da inganci, wannan ya sa manya manoma da yankasuwa ke yawan anfani da kayan kamfanin.

Sannan ya nuna matukar murna da ake shirin kafa kamfanin a karkashin manajan daraktan na Amashal Alhaji Nuradeen Hussaini Na’abba, kafa kamfanin zai samar da aikin yi ga al’ummar kasar nan musamman matasa, zai kuma kara habaka tattalin arzikin kasar nan.

Daga karshe ya ce, babban burinsa shi ne ya ga harkokin noma ya kara bunkasa da ci gaba a kasarnan musamman Arewaci.


Advertisement
Click to comment

labarai