Connect with us

LABARAI

2019: Obasanjo Ba Allah Ba Ne —Atiku

Published

on


Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya wofantar da barazanar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi masa na cewa, ba zai taba zama shugaban kasa ba matukar shi Obasanjon yana raye, ya ce, ai shi ba Allah bane.

Da yake tattaunawa a wani shirin BBC Hausa ranar Asabar, Atiku ya ce, bai taba damuwa ba a duk lokacin da ya ji Obasanjo yana irin wadannna maganganun.

Ya ce, tsohon shugaban kasan ba Allah bane, ya kuma kara da cewa, in har Allah ya kaddara zai zama shugaban kasa babu wanda ya isa ya kalubalanci kaddarar Allah.

Tsohon shugaban kasan ya tabbatar da cewar, lallai kwanaki an hana shi izinin (Bisa) shiga kasar Amurka, “Amma bayanin da suka yi mani shi ne wai sun hana ni izinin ne saboda takardar neman izinin dana mika bai bi ta hanyar data dace ba.

Da aka tambaye shi yadda zai iya zama shugaban kasa ba tare daya ziyarci kasar Amurka ba, Atiku ya ce, shin wai dole ne sai mutum ya je kasar Amurka kafin ya zama shugaban kasa? Ko kuma a kwai wani tanadin kundin tsarin mulki daya samar da haka?

‘Lallai ina iya zama shugaban kasa ba tare da na shiga kasar Amurka ba” inji shi.

Atiku ya kara haske a kan badakalar gidansa da ka ce anyi gwanjonsa a kasar Amurka kwanakin baya, ya ce, gidan da ake magana a kai ba nasa bane, na matarsa ce. Ya ce, ‘Dukkan mata na da gidajen kansu, wannan gidan da ake magana a kai na daya daga cikin mata na ne, ta sayar da gidan ne ba gwanjonsa a ka yi ba kamar yadda a ke yada wa”

Ya kuma kara da cewa, matsalar da aka samu tsakaninsa da shugaban kasa ya samo asali ne saboda rashin tafiyar da abubuwa da shugaba Buhari ya kasa a wajen tafiyar da jam’iyyar APC”

“Bayan babban zabe shekarar 2015, na sadu da shugaban kasa na yi masa bayanin cewar harkokin jam’iyya sun durkushe a kwai kuma bukatar sake fasalin jam’iyyar na kuma ba shi shawara a kan yadda zai tafiyar da gwamnatinsa na kuma yi masa bayanin cewa, in har harkoki suka ci gaba da tafiya a haka zan fita daga jam’iyyar, amma Buhari ya yi kunnen uwar shegu ya yi biris

“Idan ‘yan Nijeriya zasu iya tuna wa, mu muka kirkiro da hukumar EFCC. Nine na fara nemo kudaden da hukumar ta fara aiki da shi, sai gashi a wannan gwamnatin wasu mutane na abin da suka ga daman a karya doka amma sai gashi gwamnati na basu kariya. In har na zama shugaban kasa ba zan ba wani kariya ba matukar ya karya doka, a lokacin da muke mulki babu wani dan uwa na da aka taba samu a hannu a cikin wani almundahana.

Ya kuma kara da cewa, in har ya zama shugaban kasa, zai yi kwakwarar binciken shekara 8 da wannnan gwamnatin tayi da kudaden data kashe a yakin data keyi da kungiyar Boko Haram. ‘In na zama shugaban kasa zan binciki yadda gwamanti ta kasa murkushe ‘yan Boko Haram, gwamnatin tarayya ta murkushe yakin basasa a cikin wata 30 amma ga shi shekara 8 kenan an kasa murkushe ‘yan yaran da basu da cikakken horo.


Advertisement
Click to comment

labarai